Zan Fasa Kwai Complete hausa novel

Rate this post

zan fasa kwai complete hausa novel,zan fasa kwai hausa novel complete,Zan FASA kwai Hausa novel,zan fasa kwai,zan fasa kwai 15,zan fasa kwai page 3,littafin zan fasa kwai,zan fasa kwai hausa novel,Zan FASA kwai

Zan Fasa Kwai Complete Hausa Novel

 

ZAN FASA KWAI Complete
Name ZAN FASA KWAI Hausa novel
Size 1MB
Author Hadiza Barau Gidan Iko
File Type Apk
uploader Examdubs Novels
ebook compiler Bakori TV
date modiied Feb 2, 2022
Tags zan fasa kwai,zan fasa kwai 15,zan fasa kwai page 3,littafin zan fasa kwai,zan fasa kwai hausa novel,Zan FASA kwai

 

Ga Kadan Daga cikin  littafin Zan Fasa Kwai

Da sunan Allah me Rahama da jinkai ina godiya ga Ubangiji da ya yarda Zan fara sabon littafi na me suna ZAN FASA KWAI Ubangiji ka tsareni rubuta abinda ya kauce da tuntuben alkalami kasa ya zamo wa azi da izna_

Gaisuwa ga masoyan GIDAN IKO na kusa da na nesa Ina gaishe ku

Sai Uwata haj Saliha abubkar abdllh Zaria gaisuwar ta muddin Rayuwa ce Allah ya dafa

“Talai Wai Ina Talai ta shige don tsohon wulakanci ta barni ina ta yage bakin kiranta?

Tsohuwar ta taho da sauri tamkar zata kifa saboda Jin Kiran uwar gijiyar ta akalla tsohuwar zata haurawa shekaru sittin koma fiye ta taho da sauri har tana cin tuntube kadan ya rage taci da kasa. Ta wurgo Mata harara lokacin da take zubewa agabanta.

Zan Fasa Kwai Hausa Novel complete document

“Gani hajiya kiyi hakuri Ina bandaki naji kina Kira tun jiya Wallahi ciki ke murda min sai faman zagayawa nake…… “Ai nayi Zaton samun wuri ne yasa Kika fara nuna min kinaji Ina kwakwazon kiranki kikayi min kunnen uwar shegu dama ba Dole ciki ke rude Miki ba komai Kika samu wawab kin abkawa ciki sai kace jaka.

Wani Abu ya daki zuciyar tsohuwa talai Jin Wai yau ita take Kira da jaka Amma ya ta iya tunda Ubangiji ya zano abincinta akar Kashin wannan Mata me masifar izza wadda ko saboda izzar tata ne ma aka rada Mata suna da izzatu? Ta katseta da wata tsawa tamkar zata fasa Mata dodon kunnen “Da Allah Ni tashi ki Kai min jakata mota Kika sakani gaba kamar kin samu wata TV” Tsohuwar ta Mike da azama ta dauki jakar ta hannu wadda Isa da izza ke Hana Mata dauka Wai sai an Kai Mata duk in zata fita.

Hausa Novel complete

Tabi bayan tsohuwar tana sababi inda tsohuwar kamar zata fashe da kuka saboda Jin abinda ake fada Mata ba Diya ba jika ma tayi da ita Amma saboda kawai tana Yar aiki sai ake sauke Mata kowane kalar wulakanci tamkar ita ta kawo talauci duniya.

Ta bude mota ta saka Mata jakar ta juyo zata dawo ciki inda ta maido ta. “Na sallame ki ne kike kokarin juyawa? Wai talai me kike daukar kanki ne a gidan Nan? Akwai gadon tsohonki aciki ne? Tsohuwar ta rusuna tana Bata hakuri “Nace akwai gadon tsohonki aciki? “A a Babu hajiya na tuba ki yafe Ni nayi Zaton kin sallame Ni ne Amma ba Zan sake ba .

Ta wurgo Mata harara “Idan na dawo na samu wankin tile din Bai fita ba sai kin sauya shi wallahi duk wata sai an biyaki kudinki Amma saboda kin kware a ha inci wankin tile ma sai kinyi cuta “Zan kiyaye hajiya adawo lafiya Taja tsaki taja motar ta fice tana sababi Tsohuwa talai ta juyo ta soma aikin wankin tile tamkar zata sabunto shi yadda ya faro har dai ta tabbatar ya fita kafin ta Kama wankin kayan hajiyar inda Kuma ciwon cikin da tayi magana ya kayar da ita abin tausayi tsohuwar amai da gudawa ya sarketa ta Fadi Kan shinfida tana kwara amai zawayi na bin shimfidar inda harira ta me aikin girka abinci ta kawo Mata agaji da Dan ruwan gishiri ta Kuma tsabtace tsohuwar cikin ikon Rabbi Kuma amai da zawayin ya tsaya sai dai ta kwantsame Abu ga tsoho amai da zawayi ba Dadi Sai San maraice hajiyar ta dawo inda ta iske talai akwance Babu lafiya Amma sai me?

Zan Fasa Kwai Hausa Novel

Sai sababi da masifa Wai lambone musamman da taga wankin da talai din ta fara ciwo ya kaita kasa Aiko ta SHIGA zubar da ruwan tijara Wai akan Dole sai talai ta taso ta wanke Mata kayanta Harira ta kalleta “kiyi hakuri hajiya wallahi Bata da lafiya kwance ta wuni amai da gudawa ke damunta Bari Ni na karasa wankewa……

Ta zabgowa harira wata ashar “Na tambaye kine gwana yar ka iya?

Kauce daga Nan ko yanzu ranki yayi Baki Yar iska me shiga shirgin wani…. Tsohuwa talai ta taso tana daura Dan kwalinta ta fito dai dai da shigowar hajiya Mama uwar me gidan wadda tazamo dodan izzatu saboda masifarta Tsohuwa talai ta Yi Mata barka da zuwa inda izzatu ta Sha jinin jikinta Hajiya Mama ta amsa inda take duban talai. “Baki da lafiya ne talai?

Wallahi kuwa hajiya amai da gudawa ne…. Ta dubi izzatu fuska ahade tasoma zazaga masifa… “Kuma shine saboda Rashin sanin kimar Dan Adam bakiyi tunanin kaita Asibiti ba saboda ba uwar ki bace? Ke Wai wace irin Yar iskace ne ?

Maza ki sa akaita Asibiti ko ruwa akara Mata me aiki Ba baiwa bace sun taimake ki ba kadan ba tunda ke agidan ku Basu koya Miki komai ba “Kiyi hakuri hajiya Bari asa akaita ko kyamis ne….. “Asibiti za akaita ke in kinji naki ciwon kyamis kike zuwa?

 

Talai tace hajiya ai naji sauki ma ba sai munje ba….. “A a talai kuje ko ruwa akara Miki Baki ga yadda Kika kwaltse ba? Haka ko akayi direba ya dauki talai zuwa Asibiti inda aka Kara Mata ruwa da magunguna suka dawo gida Inda hajiya Mama ta balle hancin tsiyar da ya kawo ta gidan Dan nata “Ina da labarin duk irin cin Kashin da kikewa masu aiki izzatu kin mace ko wacece ke?

Don me Zaki samu mutane kiyi ta cin zarafin su don kawai suna muku aiki? To Bari kiji abinda ya kawo Ni gidan nan yau shekarar ki goma Sha biyu Nan gidan Amma ko batan wata bakiyi ba to na gaji da gafara sa Banga kaho ba a yau nazo da magana wadda zanyi akan ke da mijinki don haka maza ki Kira min shi yazo yanzu Ina jiran shi.

 

 

DOWNLOD

3 Trackbacks / Pingbacks

  1. Silar Fyade Hausa Novel Complete - Examdubs
  2. Saran Boye Complete Hausa Novel - Examdubs
  3. Littattafan hausa novel complete: guda 100 - Examdubs

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*