Yan Nigeria ne Matsalar Kasar nan – Buhari

 

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ce ba bambancin addini ko ƙabilanci ne matsalar ƙasar ba, mutanen ƙasar ne matsalarta.

Ya faɗi hakan ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin ƴan ƙungiyar Muhammadu Buhari/Osinbajo (MBO) Dynamic Support Group, da ke goyon bayan shugaban da mataimakinsa, a ranar Larabar nan.

A wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kan harkokin yaɗa labarai Femi Adesina ya fitar, Buhari ya ce “kanmu za mu zarga idan aka zo batun halin da Najeriya ke ciki, saboda irin rashin adalcinmu.”

Sanarwar ta ce ƴan ƙungiyar sun kai wa Buhari ziyara ne don gabatar masa da kundin irin nasarorin da aka samu a tsawon shekara biyar na mulkinsa.

A yayin da shugaban ke ganawa da ƴan ƙungiyar, ya yi waiwaye kan irin fadi tashin da ya shafe shekaru yana yi don ganin an yi masa adalci a zaɓukan da yake da yaƙinin ya yi nasara a cikinsu.

Ya bayar da misali da cewa a zaɓukan 2003 da 2007 da kuma na 2011, duk mutanen da suka ƙi yi masa adalci ƴan ƙabilarsa ne kuma addininsu ɗaya.

Yayin da waɗanda suka tsaya masa kai da fata kuma suka kasance ƴan wata ƙabilar daban kuma addininsu ba ɗaya da shi ba.

“Matsalarmu ba ƙabilanci ko addini ba ne, mu ne matsalar kanmu,” in ji shugaban.

One Comment on “Yan Nigeria ne Matsalar Kasar nan – Buhari”

Leave a Reply

Your email address will not be published.