‘Yan bindiga sun yi awon gaba da mutum 11 a unguwar Chaza da ke wajen garin Suleja a Jihar Neja.
Kakakin ’yan sandan Jihar Neja, CSP Sani Badarawa ya tabbatar da faruwar lamarin.
Mazauna sun shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar sun yi garkuwa da wani limami da wasu mutum 10 daga gidajensu.
- ‘Yan bindiga sun kwashe ‘yan Maulidin kasa dake hanyar zuwa Sokoto
- Yanda wani saurayi ya rikawa Budurwarsa karyar cewa yana da katon gida amma bayan aure taga a Kango yake zaune
Da suke bayani, mazauna garin na zargin dakatar da ayyukan ’yan sa-kai a garin ya ba wa maharan damar kai farmakin.