‘Yan bindiga sun kwashe ‘yan Maulidin kasa dake hanyar zuwa Sokoto

‘Yan bindiga sun kwashe ‘yan Maulidin kasa dake hanyar zuwa Sokoto

– An gano cewa ‘yan bindigan sun kwashe fasinjoji masu yawa a hanyar Kankara zuwa Sheme

 

– Duk da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ya musanta, mazauna yankin sun tabbatar

 

Fasinjoji dake kan hanyarsu ta zuwa Maulidin kasa dake jihar Sokoto sun shiga hannun masu garkuwa da mutane a kan hanyar Kankara zuwa Sheme dake jihar Katsina.

 

Majiyoyi da dama a yankin sun sanar da cewa basu san yawan wadanda aka sace ba yayin da jami’an ‘yan sanda suka ce babu wanda aka sace.

 

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, wasu majiyoyin sun ce an sace mutum 70 inda wasu suka ce fasinjoji 50 ne aka yi awon gaba dasu.

A wani labari na daban, a ranar Juma’a ne jihar Kaduna ta tashi da mummunan labarin sace dalibai mata a kwalejin harkar noma da gandun dabbobi da ke Mando a jihar Kaduna.

Makarantar na da nisan kasa da kilomita 15 daga makarantar horar da hafsoshin soji dake Kaduna (NDA).

 

A ranar Alhamis ne ‘yan bindiga suka kai hari kananan hukumomin Igabi, Giwa da Chikun inda suka halaka mutane bakwai. An gano cewa ‘yan bindiga sun raunata wasu tare da sace shanu 20.

3 Comments on “‘Yan bindiga sun kwashe ‘yan Maulidin kasa dake hanyar zuwa Sokoto”

Leave a Reply

Your email address will not be published.