Yan Bindiga sun Kai hari,Sun yi Garkuwa da Dan Kasuwa a Kano

Yan Bindiga sun Kai hari,Sun yi Garkuwa da Dan Kasuwa a Kano

 

Mazauna karamar hukumar Dambatta ta jihar Kano sun tabbatar da cewa wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kai musu hari tare da garkuwa da wani attajirin ɗan kasuwa a yankin.

Ganau sun tabbatarwa da BBC cewa lamarin ya faru ne da karfe 10;30 na daren Alhamis a garin Kore da ke karamar hukumar, inda suka rinka harbe-harbe kan mai uwa da wabi.

Sun kuma shaida cewa ƴan bindigar da suka kai hari sun kai mutum shida a kan babura uku. Babu dai asarar rai amma an jikkata wani yaro da harsashin bindiga a kunne.

Ƴan garin sun ce lokacin da aka kawo musu harin babu jami’an tsaro da suka kawo musu dauki ko suka zo gurin da al’amarin ya faru.

 

 

Acewarsu mutane da dama sun shiga kaduwa sannan akwai wadanda suka tsere dazuka saboda karar harbe-harben.

Shugaban karamar hukumar Dambatta Muhammad Abdullahi Kore ya tabbatar wa BBC kai harin, sannan ya shaida wanda aka sace a matsayin Emmanuel wanda ke harkokin kasuwancin sa a garin na kore.

Wannan al’amari dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ke kokawa da yadda yan bindaga ke taruwa a dajin Falgore a matsayin mafaka, inda ya nemi rundunar sojin Najeriya da su kawo masa dauki wajen ganin yan bindigar basu yi tasiri ba a jihar.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.