Yadda Zaka cika Sabon Covid19 Loan daga Babban Bankin Nigeria Ta Hannun Nirsal Micro Finance Bank

Yadda Zaka cika Sabon Covid19 Loan daga Babban Bankin Nigeria Ta Hannun Nirsal Micro Finance Bank

 

Daga Ahmad el-rufa’i idris

Sabon shiri Daga babban Bankin Nigeria ta Hannun NIRSAL Micro Finance Bank da aka yi launching Jiya Juma’a 27th August 2021.

 

Tsari ne da za’a bada bashi (loan) wa mutane domin inganta rayuwarsu kuma babu Kudin Ruwa acikin bashin (non interest Loan)

 

Program Din Ya kasu kashi uku ne Gasu Kamar haka:

 

  • HOUSEHOLD : Shiri ne na gama garin Mutane, Wanda kowa zai Iya cikawa (Maza da Mata).

 

Idan mutum ya cika Wannan Tsarin zai iya samun Kudi Naira Miliyan Daya (1M) zuwa Ƙasa.

 

  • SME: Shi Kuma wannan wani tsari ne da zai bawa masu ƙananan masana’antu damar bunƙasa Kasauwancinsu.

 

Idan Zaka cika Wannan Tsari ka Tabbatar Kanada abububuwa kamar Haka:

 

– CAC Certificate,

– Certificate of Incorporation

– Certificate of Business Name

 

Ida Ka cika Wannan Tsarin zaka iya Samun Naira Miliyan biyu da Dubu dari biyar (2.5M)

 

  •  AGSMEIS: Shi Kuma wannan tsarine wadda za’a koyar da masu masana’antu dabarun kasuwanci na zamani, sannan Kuma a basu ranchen kayan aiki wadda darajar kudin su Kimanin Naira Miliyan Biyar (5M).

 

Shi wannan tsari na AGSMEIS yanada wassu dan process wadda ya hada da training, rubuta business plan, interview kokuma online Test.

 

Dayawan Mutane zasu tambayi?

 

Babu kudin ruwa ko kadan cikin wannan tsari.

Idan ka taɓa cika wasu program na COVID-19 na NIRSAL Microfinance Bank a baya, Amma baka samu ba, toh zaka iya cika wannan. Amma, I dan ka samu previously, bazaka cika ba.

 

Babu bukatar collateral ko Kuma wani guarantor.

 

Sannan Kuma Babu bukatar kayi uploading na wani document ko hotonka. Illa iyaka BVN dinka ake bukata.

 

Zaa rufe cika wannan program din in d next 6 weeks inshallah. Amma fah Kar Ku manta, cikawa da wuri na iya baka daman samu na farko-farko wato 1st come 1st serve

 

DOMIN CIKAWA SAI ASHIGA LINK DAKE ƘASA

 

http://nibloans.nmfb.com.ng/noninterestlendingtcfhousehold

 

Yan’uwa ganin ba a jima da fara cikawa ba yakamata a sanar da al’ummarmu su cika wannan abin tun kafin ayi yawa, hakan zai bamu damar zama gaba gaba na farkon cikawa.

 

ITEM DESCRIPTION

ma’ana abinda zaka saya na sana’ar ka.

 

UNIT

Yana nufin guda nawa kakeso misali a description kasaka generator. To a unit sai ka saka guda daya kakeso ko sama.

 

UNIT PRICE

Yana nufin nawa ne wnn generator din kudinsa sai ka saka.

 

Wannan shine zai Basu damar suga nawa kake bukata a matsayin bashi. Iya yawan kayan daka saka iya yawan kudin Amma ka lissafa Kar kudin ya haura miliyan daya idan household ne idan kuma sme ne Kar kudin kayan ya haura miliyan biyu da rabi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.