Yadda na yi gudun-famfalaki safiyar yau Asabar a hanyar gona ta –Shehu Sani

Sanata Shehu Sani ya bayyana yadda ya ga wasu gungun mutane su na gudu bakin rai bakin fama a hanyar gonar sa, har shi ma ya shiga cikin su, kowa ya yi gudun tsira da ran sa.

 

Tsohon Sanata Shehu ya bayyana yadda lamarin ya faru a yau Asabar, a kan hanyar zuwa gonar sa.

 

Cikin wani bayani da ya wallafa da Turanci, a shafin sa na Facebook da karfe 11:56 a ranar Asabar, Shenu Sani ya bayyana yadda lamarin ya faru, inda ya ga mutane na gudu kamar ran su zai fita:

“Ina kan hanyar zuwa gona yau Asabar da safe, kuma ni da kai na ke tuka mota ta, can sai na hango gungun mutane kowa na ta falfala gudun tsiya. Kuma dukkan su sun nufo daidai inda na ke.

 

“Amma duk wanda ya zo daidai wuri na, sai ya zarce babu mai tsayawa, ballantana ya yi wa wani wai shi Sanata guda sukutum kama ta bayanin abin da su ke wa gudu, ko abin da ya biyo su.

 

“A na haka wata mata na zuwa kusa da ni, sai cewa ta yi, “sai ka tsayi ka yi ta tambaye-tambaye.”

 

“Ai ina jin haka, da na fizgi mota a guje, ba na jin direbobin tseren-gudun-famfalakin ‘Formula One’ za su iya kama ni.”

 

Shenu Sani ya yi wannan bayanin abin da ya ritsa da shi ne kwana daya bayan ya yi hira da gidan talbijin na CNN, inda ya yi masu karin haske dangane da matsalar yawan garkuwa da dalibai da ake yi a Arewacin Najeriya.

One Comment on “Yadda na yi gudun-famfalaki safiyar yau Asabar a hanyar gona ta –Shehu Sani”

Leave a Reply

Your email address will not be published.