Virginia Torrecilla ta dawo taka Leda bayan fama da jinya

 

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Atletico Madrid, ta mata ta sanar da dawowar ‘yar wasa Virginia Torrecilla , ɗaukar Atisaye.

Hakan na ƙunshe a cikin sanarwar da tawagar ta wallafa a shafin ta na Internet, tare da hotunan ‘yar wasan tana Atisaye.

 

Dawowar ta Torrecilla , na zuwa ne ,shekaru biyu bayan da aka fara yi mata maganin cutar Sankara (Cancer ), ta ƙwaƙwalwa , da ta kamu da cutar a baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.