Tubali Hausa Novel By Aisha Aliyu Garkuwa

Tubali Hausa Novel By Aisha Aliyu Garkuwa

Tubali Hausa Novel By Aisha Aliyu Garkuwa

Tubali Hausa Novel By Aisha Aliyu Garkuwa: On this page you will be able to read tubali hausa novel,tubali hausa novel book 2,tubali hausa novel by aisha aliyu garkuwa,tubali hausa novel page 20,tubali hausa novel wattpad,tubali hausa novel book 3,tubali hausa novel by aisha garkuwa,tubali hausa novel page 44,tubali hausa novel page 1,tubali hausa novels complete

Tubali hausa novel Description

Tubali Hausa Novel By Aisha Aliyu Garkuwa

 

Novel Title Tubali Hausa Novel
Author Aisha Aliyu Garkuwa
File uploader Novels.Zamgist
File Size 800kb
Price Free
Tags

 

DOWNLOAD

Tubali Page 1 Na Aysha Aliyu Garkuwa

Alhamdulillah Allah na gode maka da ka bani rai da lfy da damar fara rubuta wannan littafin nawa mai suna.

TUBALI: Ya Allah ka bani aron rai da lfy da konciyar hankali ka bani ikon rubutashi har ƙarshe bisa, lfy al’farmar Annabi da al’ƙur’ani. Allah kayi min tsari da abin hani, ka tsare min hannuna, tunanina, idanuna, al’ƙalamina, yatsuna, da rubuta wani abu da zai zamewa al’ummar Annabi sharri ko ya zama cutarwa ga tarbiyarmu.

GEMBU MEMBILA Taraba State.

Wani irin hadari mai masifar ƙarfi da duhu ne, ya yiwa illahirin yankin Gembu Membila ƙawanya tako wani sashi, gabas da yamma kudu da arewa yake ta gangami.

Yayinda Ya haɗe da duhun dare mai gauraye da duhun damina.

Hakan yasa babu abunda ke tashi a yankin sai wasu irin tsawa da rugugin da aketa yi babu ƙaƙƙautawa, kana kuma wata iriyar iska mai ɗan karen ƙarfi da sanyi ne ke ci gaba da kaɗawa da ƙarfi.

A dai-dai ya irin wannan lokacin kuma gaba ɗaya bani Adam mazauna cikin gidaje, sunyi nisan bacci kasan cewar ƙarfe ɗaya na dare ta gota.

Wata kyakkyawar mota ce mai masifar kyau da tsadar gaske, wanda take nuni da mamalakinta wani ne ko wane, ta faso kai.

Gudu yake shararawa cikin motar tamkar zai tashi sama.

Ma’ana gudu irin na ceton rai, shiyasa shi kansa bai san irin tuƙin da yakeyi ba.

Gaba ɗaya jikinsa kyarma yakeyi, duk da azabebben sanyin yanayin wurin, da kuma sanyin A/C’n dake cikin motar, amma hakan bai hanashi haɗa fitinanniyar zufa ta fargabar ganin alamun rabuwa da rayuwar duniya ba.

Tuƙi yakeyi yana juyowa yana kallon wata zungureriyar tirela dake biye dashi a baya, haikan-ƙadaran.

Da nufin bi ta kanshi ya takeshi, ya gane hakane ganin duk inda yayi binshi tirelar takeyi tana binshi.

Cikin tsananin tashin hankali yasa hannunshin ya sharce zufan goshinsa, kana yasa hannunshi ɗaya ya ruggume yaron dake bisa cinyarsa, yana karkarwa ganin irin azabebben gudun da sukeyi.

Dai-dai lokacin kuma suka iso, kan babban tsaunin dake saman zuzzurfan kwazazzaɓan kogin Gembu wanda yake haɗe da kogin. Numan Adamawa. Dadin Kowa Gombe. kana da binuye.

Sannan hanyar tana nan tamkar tafiyar macijiya ziz-za.

Wayarshi ya zaro a cikin kiɗima ya fara magana da wanda ya kira ɗin, yana maganar muryarshi na rawa, magana irin ta ban kwana da duniya da barin wasiyya da bada amana.

Sun zo gab da Rugar Rumo dake ƙasan hanyar can gefen kwazazzaɓan.

Dai-dai lokacin kuma, tirelar nan ta cim mishi.

Cikin tsananin mugunta ya danna motar da ƙarfi, ya ingizata, cikin ramin dake haɗe da manyan Koguna wanda zurfinsa ya zarta zaton mai zato.

Ji kakeyi k’uuuuuuhhhh, motar ta bada wani irin gigitaccen sauti.

Sai kuma ta ɗan tsaya daga gangarawar sabida karon da tayi da wata bishiya hakan yasa bata faɗa ciki kai tsaye ba.

Da ƙarfi ya kuma matsowa ganin bishiyar ta ƙare ƙaramar motar.

Ingizata yayi ta tafi cikin ramin.

Ji kakeyi fuuuuuuhhh zinɗim! Ta faɗa cikin ruwa.

Wanda sautin faɗawan yasa mafi akasarin mutanen Rugar Rumo farkawa.

Suna al’hini da tausayin sanin duk wanda ya faɗa ciki ya faɗa ƙabarinsa kenan…

Shi kuwa mai tirelar wani irin masifeffen dariya mara daɗin amo, yayi kana ya wuce cikin garin dan babu damar yin kwana a wannan wurin.

Also Read:

Kwarata Complete Hausa Novel by Jamila Musa

Littattafan hausa novel complete: guda 100

A gidanmu take complete hausa novel

Jarababben Namiji Complete Hausa Novel

Leave a Reply

Your email address will not be published.