Tsaro: Wata Kungiya ta Karrama Ganduje

Wata Kungiya ta Karrama Ganduje

 

An yaba da kokarin Abdullahi Umar Ganduje na fadadawa da bunkasa aikin dan sanda a cikin al’ummar jihar Nan ta Hanyar Sanya al’umma Cikin al’amuran tsaron Kano.
, Agenda na rundunar ‘yan sanda ta’ yan sanda ta nada gwamnan jihar Kano, a matsayin mai kula da kungiyar na kasa.

Sakataren kungiyar Kyautata alaka tsakanin Yan Sanda da al’umma ta kasa, Ambasada Ibrahim Baka Aboki ne ya bayyana hakan lokacin da kungiyar ta kasa ta kai ziyarar ban girma ga gwamnan, a gidan Africa House, gidan gwamnati, Kano, ranar Laraba, yayin taron majalisar zartarwar jihar.

A lokacin da yake gabatar da lambar yabon, Amb. Aboki ya ce “Wannan mutum ne mai gaskiya, haziki kuma mai son ci gaban kasa kuma mai son cimma burin daya sanya a gaba Kuma Gwarzon ta fuskar tsaro. Muna gabatar maka da wata kyauta da kuma Lambar yabo a matsayinka na Uban Wannan Kungiya ta Kasa.”

Ya ce “Gumuna a gaban Mai Girma, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da majalisar Zartarwar sa don gabatar da shaidar girmamawa ta hannun rundunar ‘yan sandan Sarauniya Kuma Shugaban Kyautata alaka tsakanin yan sanda ta kasa da ke karkashin jagorancin DCP / SC Muhammad Bello Dalha.”

A lokacin da yake bayani game da aikin gina Nijeriya da gwamnan yayi, ya ce Ganduje Yana aikin sosai da nufin inganta haɗin gwiwar ‘yan sanda na al’umma, magance matsaloli tare da sauya tsarin ƙungiyoyi.

Don haka mun yarda da mahimmiyar rawar da Ganduje yake takawa a fagen hidimar Samar da tsaro a Kano,da kuma inganta dukkan tsare-tsaren tsaro, hukumomin tsaro, na musamman (CPOs) da dai Sauransu.

A jawabinsa, gwamna Ganduje ya ce, “Abin da muke yi a Kano shi ne, lokacin da muke fuskantar kalubale, mun mayar da su dama bamu Bari kalubalen ya Kai mu Kasa ba.”

Ya ce “Mun fara ne da inganta alakar ‘yan sanda da fararen hula, sannan muka zo ga aikin’ kyautata alakar yan sanda na Sauran Hukumomin tsaro. Muna da aikin Samar da tsaron al’umma a matakai daban-daban, wato matakin kauye, matakin unguwanni, matakin karamar hukuma, matakin Masarautu da kuma na jiha”.

Don kara nuna irin jajircewar da jihar ke yi wajen karfafa aikin dan sanda, ya bayyana cewa, “Baya ga matasa 16 da muka zaba daga kowace karamar hukuma daga cikin kananan hukumomi 44 don samun horo na Constabulary, muna da wasu wadanda su ma ake yi wa irin wannan horo. “

Ya bukace su da su yi amfani da damar da suke da ita don inganta tsaron jihar nan da ma kasa baki daya, yana mai nuni da cewa, “Mun sanya tushe mai kyau don Samar da kyakkyawan tsaron jiharmu.”

Leave a Reply

Your email address will not be published.