Muna muku maraba da zuwa wannan shafin namu Mai albarka Inda Muka kawo muku Tarihin Jaruma hafsat Ahmad Idris wato hafsat Idris wadda aka fi sani da suna “barauniya”.
Tarihin Hafsat Ahmad Idris (hafsat Idris)
Fitacciyar jarumar Kannywood Hafsat Idris ta shahara wajen fitowa a wani fim mai suna “Barauniya” An haifi fitacciyar jarumar kannywood ranar 14 ga watan Yuli 1987 a karamar hukumar Sagamu ta jihar Ogun ga iyayenta.
Ta yi karatun firamare da sakandare a jihar kafin ta shiga harkar. Hafsat ta kasance ‘yar kasuwa a da, amma saboda sha’awar da ta ke yi na yin fim ta daina sana’ar ta ta shiga masana’antar fina-finan Kannywood.
Jarumar dai ta samu damar shiga harkar ne a shekarar 2016 kuma ta samu damar yin fim tare da manyan jaruman kannywood irin su Ali Nuhu da Adam A Zango. Fim dinta na farko mai suna “Barauniya” ya sanya ta shahara a Najeriya.
Tun da ta shiga masana’antar, Jarumar ta fito a fina-finan Kannywood sama da 50 da suka hada da, Barauniya, Rariya, Risa, Igiyar Zato, Wacece Sarauniya, Zan Rayu Dake, Fim din Yarda da dai sauransu.
Fim din ya ci gaba da samun lambobin yabo da nadiri da dama a waccan shekarar, wasu daga cikin lambobin yabo nata, ta lashe kyautar jarumar da ta yi fice a kyaututtukan nishadi na birni a shekarar 2018, Hafsat ta sake lashe kyautar jarumar fim a 2019 a lambar yabo ta birnin City.
Kadarar Jaruma Hafsat Idris
Kyakyawar jarumar Kannywood Hafsat Ahmad Idris wacce aka fi sani da Hafsat Idrisi tana da kimanin dalar Amurka dubu Dari hudu $400,000 kwatankwacin Naira Miliyan 160,000,000 akan Naira 400 na kudin Najeriya kan kowacce Dala.
Hotunan Jaruma Hafsat Idris

Hafsat Idris Instagram
Zaku iya biyar shafin jarumar dazarar Kun dannan Wannan koren rubutun – Instagram
Wasu daga Cikin Fina finan Hafsat Idris
- Mace Mai Hannun Maza 2016
- Wazir 2016
- Gimbiya Sailuba 2016
- Matar Mamman 2016
- Risala 2016
- Igiyar Zato 2016
- Wata Ruga 2017
- Rariya 2017
- Wacece Sarauniya 2017
- Zan Rayu Da Ke 2017
- Namijin Kishi 2017
- Rigar Aro 2017
- Yar Fim 2017
- Dan Kurma 2017
- Kawayen Amarya 2017
- Dr Surayya 2018
- Algibla 2018
- Ana Dara Ga Dare Yayi 2018
- Mata Da Miji 2019
Daga Karshe Muna fatan Kunsamu bayanin dakuke nema gameda Jarumar Kannywood hafsat Ahmad Idris. Idan kana KO kina da wani abunda zakuce, toh zaku iya rubutawa ta comment.