Ta Kashe Jaririyarta, Ta Jefa Gawar A Kogi

Jami’an ’yan sanda sun cafke wata mata mai bisa zargin kashe jaririyarta ’yar wata daya tare da jefa gawarta a cikin kogi.

 

Dubun matar mai shekara 35 ya cika ne bayan ’yan sanda da ke sintiri daga caji ofis din Enugada sun titsiye ta bayan sun yi sun yi tantama da suka ga tana jefa wani abu a cikin kogi.

Kakakin ’yan sanda a Jihar, Abimbola Oyeyemi, ya ce, da ’yan sandan suka ji ba su natsu ba, nan take suka damke ta suka shiga yi mata tambayoyi.

Oyeyemi ya ce, “A wurin binciken ne ta bayyana cewa gawar jaririyar da ta haifa wata daya da ya wuce ne ta jefar, kuma tsananin damuwa ya sa ta kashe jaririyar.

 

“Ta ce wanda ya yi mata cikin ne ya ki karbar ’yarsa, ita kuma da ta ga ba ta halin kula da ita, sai ta kashe ta, ta jefar a kogi,” inji Oyeyemi.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.