Shugaba Buhari Zai je Lagos

An tura jami’an tsaro da dama Legas gabanin ziyarar Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari inda zai ƙaddamar da wasu ayyukan gwamnati a yau Alhamis

Akwai fargaba a faɗin ƙasar yayin da ake sa ran gudanar da zanga-zanga ranar 12 ga watan Yuni a ƙasar wato ranar Demokuraɗiyya.

Masu fafutuka a Legas da sauran manyan birane a ƙasar na fatan yin zanga-zanga don nuna ɓacin ransu dangane da matsalar tsaro da ke ta’azzara da barazana ga ƴancin tofa albarkacin baki musamman yanzu da aka haramta Twitter.

Jaridar Punch a Najeriyar ta ruwaito cewa tawagar Shugaban ƙarƙashin jagorancin Sufeto Janar na ƴan sanda Usman Baba ta riga ta isa Legas.

Ziyara ta ƙarshe da Buhari ya kai Legas a watan Afrilun 2019 ne.

]

Leave a Reply

Your email address will not be published.