Sayyada Rabi’atu Haruna: Ana jimamin rasuwar matar da ta yi wakar ‘Mai daraja Annabi Ma’aiki’

Musulmi a Najeriya da ma wasu kasashen duniya sun fada cikin jimamin rasuwar Sayyada Rabi’atu Haruna, matar nan da ta yi fice wajen wakokin yabon Annabi Muhammad (SAW).

 

Mijinta Sharif Mu’azu ya shaida wa BBC cewa a ranar Talata ne mawakiyar ta rasu a gidanta da ke Rigasa a birnin Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya bayan ta yi jinyar mako uku.

 

Ya ce an yi jana’izarta da yammacin ranar ta Talata.

 

A cewarsa mutuwar Sayyada Rabi’atu ta yi matukar girgiza shi da iyalinsa yana mai yin addu’ar Allah ya jikanta.

Sharif Mu’azu ya bayyana mai dakin nasa a matsayin mutuniyar kirki wadda ya ji dadin zama tare da ita.

Sayyada Rabi’atu ta bar ‘ya’ya biyu a duniya.

Ta yi wakokin yabon annabi wadanda suka hada da ‘Sayyidin Nasi Karimi’, ‘Mai daraja Annabi Ma’aiki’, ‘Zahra’u Fadima’, ‘Shukriyya Sajida’, da wasu da dama.

Masu sha’awar wakokinta da ma sauran Musulmi musamman a shafukan sada zumunta sun yi matuka kaduwa da jin rasuwar mawakiyar.

Isa Usman ya bayyana kaduwarsa da rasuwar Sayyada Rabi’atu yana mai yin addu’ar Allah Ya sa ta kasance “bakuwar Muhammadur RasululLah Sallallahu Alayhi Wa Sallam.”

Shi ma Adamu Aliyu Shu’aibu ya yi mata fatan samun rahamar Allah sannan ya ce yana “kaunar wakokinta irin su ‘Na yi dace na rike soyayyar ma’aiki, da ‘Abin dogaro Muhammadu’ da kuma Karimiya”

A nasa bangaren, Bilya Hamza Dass, ya yi alhini sannan ya bayyana daya daga cikin wakokinta da ya sani.

3 Comments on “Sayyada Rabi’atu Haruna: Ana jimamin rasuwar matar da ta yi wakar ‘Mai daraja Annabi Ma’aiki’”

Leave a Reply

Your email address will not be published.