Sakon Barka Da Shan Ruwa Zuwa Ga Masoyiyata/Masoyi

Sakon Barka Da Shan Ruwa Zuwa Ga Masoyiyata Kokuna Masoyi.

Ina Mai karatu barka DA shan ruwa, Ya ibada ya kishirwa? Dafatan Allah yakarba mana ibadun mu Ameen.

A wannan shafin mun kawo muku Sakon Barka Da Shan Ruwa Zuwa Ga Masoyiyata kokuma masoyina, Wato sakunan sun kushi Na mace dakuma Na namiji.

Sakon Barka Da Shan Ruwa Zuwa Ga Masoyina

sakon barka da shan ruwa zuwa ga masoyiyata

#1. Zuwa ga zaɓin zuciyata, ina fatan kasha ruwa lafiya? Ina fatan izuwa yanzu natsuwa ta game jikinka, ishiruwa ta gushe daga makoshinka? Ina kuma fatan lada ya tabbata a gare ka. Fatan ka sha ruwa lafiya? Ka Huta Lafiya.

 

#2. A dukkan lokacin da na ga daren Lailatilkadari, zan kasance mai rokon Ubangiji Ya mallaka min kai a matsayin mijina uban ‘ya’yana, ina fatan kai ma zaka kasance mai tsawaita tsayuwa cikin kowane dare domin ganin cikar burinmu? Ina Son Ka.

 

#3. A lokuta da wurare daban-daban ina ganin ka kana yi min gizo, ina ganin ka a lokacin da idanuwana ke a rufe ko abuɗe. Ba na iya yin komai ba tare da tinaninka ba. Fatan Ka Sha-ruwa Lafiya.

 

#4. Jin muryarka na sakwan guda, na jefa ni cikin kogin tinaninka, na tsawan lokacin da idanuwana ke kasancewa abuɗe. Barka Da Shan-ruwa.

 

#5. Irin kulawar da kake nuna min a kullum na saka ni tinanin irin yadda rayuwarmu za ta kasance a nan gaba. Zanbzamo tamkar sarauniya a gidanka, kai kuma zaka zamo sarkin da babu wani mai irin masarautarsa a duniya ta kowace fuska. Ina Son Ka.

 

#6. Zuciyata ba za ta taɓa canja matsayin da kake da shi ba a cikinta. Murmushina gare ka ba zai taɓa yankewa ba. Son ka a cikin zuciyata ya yi kafuwar da ba zai taɓa goguwa ba a cikinta na har abada. Barka Da Hutawa.

Also Read: Kalaman Soyayya: Guda 100 na 2022

#7. Da a ce zan iya zama komai, da na zama ruwan hawaye a gare ka, a haife ni a cikin idanuwanka, na rayu a saman kumatunka, na mace a saman laɓɓanka. Ina son ka so mara misaltuwa. Barka Da Shan-ruwa.

 

#8. A dukkan lokacin da kake bukatar wani ya taya ka hira, karda ka manta kana da ni, ka nemo ni domin ɗebe maka kewa a cikin kowane irin yanayi da lokaci. Fatan Ka Wuni Lafiya? Yaya Ibada?

 

#9. A lokacin da na tino irin rayuwar dana yi a baya, na kan hango irin asarar da na yi, na kasancewa ta ni kaɗai ba tare da kai ba , yanzu na same ka, ina ji na a matsayin wata wadda ta fi kowace mace sa’a a rayuwa. Ina fatan na kasance a tare da kai na har abada. Barka Da Shan ruwa.

 

#10. Ba zan taɓa mantawa da ranar cikar burina ba, ranar da wanda nake so ya nuna min soyayyarsa a fili, ba kowa bane face kai hasken idaniyata. Ina son ka. Barka Da Hutawa. Fatan Ka Sha-ruwa Lafiya?

Sakon Barka Da Shan Ruwa Zuwa Ga Masoyiyata

#1. Zuwa ga zaɓin zuciyata, ina fatan kinsha ruwa lafiya? Ina fatan izuwa yanzu natsuwa ta game jikinki, kishiruwa ta gushe daga makoshinki? Ina kuma fatan lada ya tabbata a gare ki. Fatan kinsha sha ruwa lafiya? Ki Huta Lafiya.

 

#2. A dukkan lokacin da na ga daren Lailatilkadari, zan kasance mai rokon Ubangiji Ya mallaka min ke a matsayin matata uwar ‘ya’yana, ina fatan ke ma zaki kasance mai tsawaita tsayuwa cikin kowane dare domin ganin cikar burinmu? Ina Son Ki.

 

#3. A lokuta da wurare daban-daban ina ganin ki kina yi min gizo, ina ganin ki a lokacin da idanuwana ke a rufe ko abuɗe. Ba na iya yin komai ba tare da tinaninki ba. Fatan Kin Sha-ruwa Lafiya.

 

#4. Jin muryarkai na sakwan guda, na jefa ni cikin kogin tinaninki, na tsawan lokacin da idanuwana ke kasancewa abuɗe. Barka Da Shan-ruwa.

Karanta: Sakon Barka Da Safiya Na Soyayya

#5. Irin kulawar da kike nuna min a kullum na saka ni tinanin irin yadda rayuwarmu za ta kasance a nan gaba. Zanbzamo tamkar sarki a gidanki, ke kuma zaki zamo sarauniya da babu wani mai irin masarautarsa a duniya ta kowace fuska. Ina Son Ki.

 

#6. Zuciyata ba za ta taɓa canjawa a matsayin da kike da shi ba a cikinta. Murmushina gare ki ba zai taɓa yankewa ba. Son ki a cikin zuciyata ya yi kafuwar da ba zai taɓa goguwa ba a cikinta na har abada. Barka Da Hutawa.

 

#7. Da a ce zan iya zama komai, da na zama ruwan hawaye a gare ki, a haife ni a cikin idanuwanki, na rayu a saman kumatunki, na mace a saman laɓɓanki. Ina son ki so mara misaltuwa. Barka Da Shan-ruwa.

 

#8. A dukkan lokacin da kike bukatar wani ya taya ki hira, karda ki manta kina da ni, ki nemo ni domin ɗebe maki kewa a cikin kowane irin yanayi da lokaci. Fatan Kin Wuni Lafiya? Yaya Ibada?

 

#9. A lokacin da na tino irin rayuwar dana yi a baya, na kan hango irin asarar da na yi, na kasancewa ta ni kaɗai ba tare da ke ba , yanzu na same ki, ina ji na a matsayin wani wanda ya fi kowane namiji sa’a a rayuwa. Ina fatan na kasance a tare da ke na har abada. Barka Da Shan ruwa.

 

#10. Ba zan taɓa mantawa da ranar cikar burina ba, ranar da wadda nake so ta nuna min soyayyarta a fili, ba kowa bane face kai hasken idaniyata. Ina son ki. Barka Da Hutawa. Fatan Kin Sha-ruwa Lafiya?

 

Ina Rokon Allah yakarbi Ibadun mu acikin wannan wata Mai alfarma Na Ramadan. Ameen

Leave a Reply

Your email address will not be published.