Sakon Barka Da Safiya Na Soyayya

Sakon Barka Da Safiya Na Soyayya

Sakon Barka Da Safiya Na Soyayya

Sakon Barka Da Safiya: Assalamu alaiki farin cikin zuciya ta kuma sanyi idanuwana, hakika kece mace ta farko wacce na yi gamo da ita.

 

Sakon Barka Da Safiya Na Soyayya

bantaba zato ko tsammanin za’ayi wata ‘ya mace wacce zata sace min dukkanin ruhi a mafi kankantar lokaci ba sai ke,

amma sai gashi ba tsammani nayi kicibis da kyakkyawar fuskar da na kasa dauke wa kallo.

Hakika kyauwun ki yakai ayi misali dashi, kinsha gaban duk mai tinani, zuciyar ki Kyakkyawa ce, tafiyar ki mai tsari ne.

Rayuwar ki abar kallo da koyi ne, lallai nayo matukar Sa’ar samun mace kamar ki a cikin rayuwata Muradina, Annuri na, Kuma Shalelen Zuciyata.

 

—-SAKON BARKA DA SAFIYA—-

Barka da Safiya Tare dafatan kin tashi Lafiya.

Kimin uzurin ganin wannan sakon nawa tunda safe, dolece ta sanya Hakan,ina neman mafita ne, Duk da cewar Muna safiya sanyinta na kadawa,Amma hakan bai hanani daukan gumi ba.

Ina Sonki tsawon lokaci kwarjiinki ya hanani Sanar dake, duk da cewar ba laifi, bane kyaunki da ajinki suna razanar Dani ta yadda bana iya zuwa na isar da sakon sona agareki.

Nayi amfani da wannan damar na turomaki sako na a rubuce, kimin uzuri kuma ki karbi wannan sakon nawa, Hakazalika kiban dama domin tabbatar maki da wannan sakon nawa.

Kowanne dan Adam yanada dalilin kamuwa da Son wata, ko kuma son wani. Zaki so jin nawa Dallin?

zaki iya bani lokacinki aro domin zayyana maki halin da nakeciki a dalilin Sonki.

Amsarki nake jira ya wacce Sonta yayimin dabai bayi. Tare da dauramin sarka irin ta So da Kauna.

Karanta: Kalaman Soyayya Masu dadi 2022

Shawara Ga Samari ‘Yan Soyayya

 

Yi ammafani da kalaman soyayya masu Dadi da inganci a lokacin da kake Gwagwarmayar samun amincewar zuciyar Dukkan wata yarinya da ka gani kana son Mallakarta.

Kasance mai lissafawa tare da tauna Dukkan wata magana kafin ka furta ta ga Masoyiyarka bayan ta nuna maka Amincewarta a soyayyarka.

Karda ka kasance mai takura wa tare da Matsantawa a kan dole sai ta yi wani Abu da ta nuna maka bata son yi a zahiri Ko ta nuna maka alamun hakan, domin Kuwa hakan zai sanya ta fara gajiya tare Da kosawa da kai.

A dukkan lokacin da kake son ta yi Maka wani abu to ka gabatar mata da Bukatar ka cikin siyasa da zolaya amma Idan ka nuna mata dole to kuwa ba zaka Samu yadda kake so ba idan ka samu An yi ma kenan.

Kasance mai yin dukkan wani abu da ka San zai faranta mata ka kuma guji yin Dukkan wani abu da ka san zai kuntata Mata.

Yi mata kyauta a lokacin da bata Zaton samun hakan daga wajen ka, yin Hakan zai sanya ka burgeta zai kuma Kara sanya soyayyar ka a cikin zuciyar ta.

Karda ka cika yi mata kyautar kudi ko Bata wasu abubuwa barkatai domin kuwa Yawan yin hakan zai sanya ka kasa Banbance cewa soyayyar gaskiya take yi Maka ko kuma kudin ka take so.

Mace ba ta son takura, ba ta son kafiya,

Da maimaita mata abu daya, kuma ta Son ka cika kushe wani ko wata a Gabanta.

Haka zalika ba ta son a duk Lokacin da kuke tare ka rika nuna kulawa Ko fifiko ko nuna wata ta fita kyau ko Wani abu makamancin haka.

Mata suna Son ka rika yabon kyawunsu.

Sannan ka kasance mai bayyana mata Cewa ita kyakkyawa ce a duk lokacin da Kuka yi waya ko kuma kuke tare, ka rika Bayyana mata cewa muryarta na da dadi Sosai, kana samun nutsuwa a duk Lokacin da ka ji sautin muryarta, ka nuna Mata cewa ta iya kwalliya kuma tana da Tsafta.

A duk lokacin da kuka hadu a hira a Waya ko a zahiri ko sako ka tura mata to Lallai ka bayyana mata kana sonta kafin Ku rabu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.