Mutum Biyu Sun Mutu Bayan Karbar Rigakafin Coronavirus

ukumomi a Kasar Koriya ta Kudu sun fara bincike kan wasu mutum biyu da suka mutu bayan ’yan kwanaki da yi musu allurar rigakafin cutar coronavirus ta AstraZeneca.

 

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa mutanen biyu da suka riga mu gidan gaskiya bayan karbar allurar rigakafin, suna fama da wasu cututtukan na daban.

Wata tsohuwa mai shekara 63 da ke jinya a gidan masu fama da cutar kansar jini, ta kamu da zazzabi mai zafi kwanaki hudu da yi ma ta rigakafin cutar a cewar Jeong Eun-kyeong.

 

Kamfanin Dillancin Labarai na Yonhap, ya ruwaito cewa a ranar Talata ne aka mayar da wani mutum zuwa wani Babban Asibiti bayan ya nuna alamun kamuwa da cutar gurbatar jini da kuma nimoniya.

 

Haka kuma, wani majinyaci mai kimanin shekara 50 da ke fama da ciwon zuciya da ciwon sukari, ya mutu a ranar Laraba sakamakon ta’azzara da ciwon zuciyar ya yi kwana daya da yi masa allurar rigakafin cutar Coronavirus ta AstraZeneca.

 

Sai dai kamfanin AstraZeneca ya ce yana sane da binciken da Hukumar Kula da Yaduwar Cututtuka ta Kasar Koriya ta Kudu KDCA ke yi a kan rigakafin.

 

Kamfanin ya ce an yi nazari da bincike mai zurfin gaske gabanin tabbatar da ingancin rigakafin ga lafiyar al’umma.

2 Comments on “Mutum Biyu Sun Mutu Bayan Karbar Rigakafin Coronavirus”

Leave a Reply

Your email address will not be published.