Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City dake kasar Ingila ta kammala daukar dan wasa Julián Álvarez daga River Plate.
Kungiyoyin biyun tuni suka amince da sauyin shekarar matashin dan wasan a ranar Talata 25 ga Janairun 2022.
Manchester City dai ta sayi dan wasan a kan kudi fam miliyan 18.5.
Wanda hakan ya sa dan wasan zai sanya hannu a kwantaragin shekaru biyar.
Sai dai dan wasa Álvarez zai ci gaba da zama a River Plate a matsayin aro har zuwa watan Yuli kamar yadda dan jarida kuma masani a harkokin cinikayyar ‘yan wasa Fabrizio Romano]