Maganin Tsawon Gashi

Maganin tsawon gashi: Akwai hanyoyi da dama da mata za su bi domin samar da gashin kai mai tsawo.

Mata da dama suna son ganin kansu da gashi mai tsayi kamar na Indiya. Gashi na daya daga cikin ababen da ke dada wa mace kyau don haka, ya kamata mu kula da gashinmu sosai. Wannan hadin da zan rubuto muku na dada wa gashi maiko , wato yana hana gashi karyewa da sanya shi tsayi da laushi.

Karanta: Sabbin Hotunan Lalle na Zamani 2021 masu Kayatarwa

Ina son a san cewa wannan hadin akan yi shi ne kamar sau biyu a wata. Idan mutum ya kasance mai yin wani hadi ne daban wanda ba wannan ba, ba ya kamata ana hada wannan salon gyaran gashi da wani daban in ba haka ba, sai a ga kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.

 

Abubuwan da za a bukata domin Gyaran gashi

 • Man Amla
 • Zuma
 • Ruwan dumi
 • Hadi

A zuba cokalin amla biyu a roba.

Sannan sai a zuba rabin cokalin zuma a cikin amla.

A sanya cokalin ruwan dumi kamar 2-3.

A juya hadin har sai sun cakudu da juna.

A taje gashi kafin a shafa wannan hadin a fatar kai.

A jira na tsawon minti 30.

A wanke kai da man wanke gashi (shampoo).

Amfani da man kwakwa

man kwakwa na sanya gashi laushi da tsayi da kuma santsi. Yana da kyau a rika shafa shi a gashin kai duk lokacin da za a yi kitso ko kuma a rika gauraya shi a cikin man kitso.

Man zaitun

wannan man na da mahimmanci sosai a jiki baki daya. Sannan kuma yana sanya gashi santsi da baki. Yana kuma rage furfura a gashi da kuma sanya gashi tsayi da baki da sheki da kuma kyau.

Dogayen gashi tabbas abu ne da kowacce mace take son samu, domin dogayen gashi yana sa mace tayi kyau ko mace ce ko budurwa ko matar aure.

KARANTA: Maganin Sanyi Na Mara, Mata, Kashi, Maza Na Gargajiya

A baya, kamar yadda muka yi magana game da yadda ake wanke gashin ku da tabbaci, a yau za mu yi magana ne game da wasu muhimman abubuwan da ke sa dogon gashi ya zama al’ada.

Gyaran Gashi

1. Man Albasa

Man Albasa na da matukar amfani ga gashin mace kamar yadda masana suka ce yana kara tsayi da laushi har ma da kauri. Ki rika shafawa da zarar kin wanke kanki.

2. Man Hulba

Hulba ba wai kawai wani abu ne mai girma ga jikin gashi ba, har ila yau yana da kyau ga mace. A fannin gashi kuwa, ko shakka babu ana ba da shawarar sosai, musamman bayan kitso.

3. Man Kadanya

Man Kadanya yana da amfani ga jikin mace domin yana da lafiyayyan nau’in maganin shafawa na Verselen wanda muke shafawa tsawon lokaci a jikin mutum.

4. Man kwakwa

Man kwakwa yana taimakawa wajen kara tsayin gashin mace da kuma kare ta daga kamuwa da cututtuka da ke yi mata barazana.

 • Man Kadanya Kadanya man yana da matukar amfani a jikin mace domin yana da lafiyayyan nau’in maganin shafawa na Verselen wanda muke shafawa tsawon lokaci a jikin dan adam.
 • Man kwakwa na taimakawa wajen kara wa mace tsayi da kuma kare mata kamuwa da cututtuka da ke yi mata barazana.
 • Man Kwakwa Man kwakwa abu ne mai zaki ga kamfanoni da dama da ke hada man gashi.

Suna yawan hada man gashi domin yana da matukar amfani ga gashi. Kadan daga cikin amfanin shafa shi a gashi sun hada da.

 • Maganin ciwon kai
 • Yana kara kaurin gashi
 • A fuska yana magance kurajen fuska
 • Yana sa laushi gashi
 • Yana kara bakin gashi

5. Man zaitun

man zaitun shima yana da matukar amfani wajen gyaran gashi kuma yana taka rawa sosai. Ana shafa man zaitun a fatar kai yana kara tsawatar gashin da kuma kara inganta shi ta yadda zai yi laushi da santsi, sannan yana kara kwalliyar gashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.