LABARI DA DUMI DUMI: Jonathan ya ce APC ta nemi ya dawo cikinta

Jonathan ya ce APC ta nemi ya dawo cikinta

 

Tsohon shugaban tarayyar Najeriya Dakta Goodluck Ebele Jonathan, ya shaidawa duniya cewa, jam’iyyar APC mai mulkin kasar tana zawarcinsa domin ya dawo cikinta, a wata hira da ya yinda manema labarai a jihar Bayelsa dake zama mahaifarsa tsohon shugaban ya ce.

 

“Na samu maban bantan katunan gayyata domin halartar tarurrukan jam’iyyar APC amma ban je ba saboda wasu dalilai, sannan jagororin jam’iyyar na kasa suna kirana da cewa in dawo jam’iyyar domin hada kai da kai don ciyar da kasar nan gaba amma dainban gama yanke shawara ba sannan a zahirin gaskiya a halin yanzu bani da bukatar komawa a cikin jam’iyyar ta APC”.

 

Kamar yadda ya bayyana sannan bugu da kari an tambayi tsohon shugaban wato Goodluck Jonathan cewa, shin da gaske ne jam’iyyar na son dawo da shi cikinta don bashi tikitin taka takarar shugabancin kasar nan a zabe mai zuwa? – Jonathan ya ce APC ta nemi ya dawo cikinta

 

Sai ya kada baki yace ” to ni dai ban sani ba amma dai kamar yadda kuka ji wadannan rade radi nima haka nake jin su amma har yanzu babu wanda ya tunkare ni da maganar” in ji shi.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.