Kungiyar Masu Kayan Abinci Na Arewa Za Su Shiga Yajin Akin Kai Kayan Abinci Yankin Kudu

Hadaddiyar kungiyar kayan abinci na kasa tana sanar da membobinta na kasa musamman al’ummar arewacin Nijeriya cewa za ta tafi yajin aiki na sai baba tagani.

 

Kungiyar ta bayyana cewa daga karfe 12 pm na daren jiya Talata za ta tare duk wata hanya da kayan abinci, kama daga kayan gwari, shanu, awaki da duk wani nau’in nama, ko hatsi masara, dawa, shinkafa, da duk wani kayan abinci da zai bi ya wuce zuwa kudancin Nijeriya.

 

Hukuncin ya biyo baya ne sakamakon irin barnatar da dukiyan al’ummar arewacin kasar nan da ‘yan kudancin Nijeriya suke yi a duk lokacin da suka ga dama, inda suke kona motocin kayan abinci ,su kashe ‘yan arewa tare da kona shagunan ‘yan arewa. Kuma babu wani mataki da aka dauka.

Sannan duk wani memban kungiyar da ya yi kunnin uwar shegu da wannan doka, motar sa ba za ta wuce ba, kuma kayan cikin motar ya zama ganima domin a nan za a zubar da kayan.

 

kungiyar ta bada wannan sanarwa ne a taron daya gudana a jiya Talata a Abuja.

 

Ko ya kuke ganin wannan hukuncin?

One Comment on “Kungiyar Masu Kayan Abinci Na Arewa Za Su Shiga Yajin Akin Kai Kayan Abinci Yankin Kudu”

Leave a Reply

Your email address will not be published.