Jaruma Ummi Rahab (Diyar Adam Zango) Ta Bayyana Saurayin Da Zata Aura. 

[ad_1]

Jaruma Ummi Rahab wadda tun tana karama ta fito a wani fim wanda suka hau wata waka ta Nura M Inuwa tare da ita da Adam A Zango da Jamila na Gudu da kuma Haidar dan Adam A Zango

jarumar ta dawo fim da wani irin farin jini na musamman.

Kusan tun wancen fim na Ummi da aka dauka a shekarun baya ba’a kara jin duriyar wannan jaruma ba sai a wannan karon da Adam A Zango yake aikin daukar wani sabon fim mai suna ‘Farin Wata’.

Ummi dai tana daya daga cikin jaruman da suke taka rawa a wannan kasaitaccen fim da Adam A Zango ke dauka na Farin Wata ‘karkashin kamfanin sa na White House family.

A lokacin da jaruma Ummi Rahab ta dawo fim sai jama’a sukaga ta girma ta zama budurwa inda wasu da dama suke mata sha’awar aure. Domin mutane da dama suna ta yi mata addu’ar Allah Ya fito mata da miji tayi aure.

To yanzu dai jarumar da bakin ta fadawa duniya saurin da take so wanda kuma shine dan uwan Adam A Zango wato KB Zango kamar yanda zakuji daga bakin ta.

Kuma jaruma Ummi ta bayyana haka ne a gurin 2020 daukar fim din na Farin wata a yayin da Adam A Zango da kansa yake tsokanar ta cewa yayi mata miji wanda shine Jamilu kocila, wanda hakan ne kuma ya sa jarumar ta fadi abin da ke cikin zuciyar ta kamar yanda zaku gani yanzu.

[ad_2]

Leave a Reply

Your email address will not be published.