Hukuma ta ƙwace finafinan batsa a Sakkwato

HUKUMAR Tace Finafinai ta Ƙasa (National Film and Video Censors Board) ta kai wani samame tare da samun nasarar ƙwace wasu finafinan ƙasar waje na batsa da kuma marasa lasisi a garin Sakkwato.

 

Hukumar ta kai wannan samame ne tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro a cikin wasu unguwanni da ke birnin na Shehu da su ka haɗa da Titin Ahmadu Bello, Titin Emir Yahaya da kuma Titin Abdullahi Fodiyo.

 

Da ya ke zantawa da manema labarai a jiya Litinin, shugaban hukumar, Alhaji Adedayo Thomas, ya ce hukumar za ta ci gaba da kama irin waɗannan haramtattun kayayyakin a dukkan kasuwannin da ke faɗin ƙasar nan.

 

Ya ƙara da cewa hukumar za ta lalata dukkan kayayyakin da su ka kama domin ya zama izna ga wasu.

 

Zaku so kukaranta : Tabbas Rahama Sadau Tayi Kuskure Kan Sake Sakin Irin Wadannan Hotunan Da Ka Iya Jawo Mata Cece Kuce

Ya ƙara da cewa bayanan sirri sun nuna cewa Sakkwato na ɗaya daga cikin matattarar masu yaɗa irin waɗannan haramtattun ayyukan.

 

Ya lissafa kayan da su ka ƙwace kamar su dibidi da sidi irin waɗanda a kan ɗora fim fiye da guda a kan su, da sauran finafinan ƙasar waje da na gida waɗanda ba a tace su ba, ciki har da na batsa.

 

Ya ce: “Mun kai farmaki a wuraren da ake harhaɗa waɗannan abubuwan tare da shaguna har ma da wasu wuraren da ake sayar da irin waɗannan haramtattun kayan waɗanda yawancin su an kwafe su ne, sannan ba su da shaidar izini.

 

“Ba shakka, masu harka amasana’antar su na yin asarar biliyoyin naira ta hanyar ayyukan marasa inganci da fasa-ƙwauri da kuma ayyukan da ba a rarraba su ba ta hanyar wakilai da dillalai, wanda a ƙarshe hakan ke hana gwamnati samun kuɗaɗen shiga da aka gindaya.

 

“Babu shakka, ayyukan waɗannan mutane da ƙungiyoyi su na da mummunan tasiri ga al’umma, wanda hakan na sanyaya gwiwar masu ruwa da tsaki da ma masu son saka hannayen jari a masana’antar.”

 

A ƙarshe, Alhaji Thomas ya bayyana cewa hukumar sa za ta ci gaba da kai samame zuwa wasu sassan ƙasar nan, da su ka haɗa da Kano, Kaduna, Abuja, Onitsha da Aba da ke cikin Abia.

3 Comments on “Hukuma ta ƙwace finafinan batsa a Sakkwato”

Leave a Reply

Your email address will not be published.