Halilu Getso ya bayyana Dalilin da yasa ya ajiye Shugabancin Gidan Radio Jalla

Halilu Getso ya bayyana Dalilin da yasa ya ajiye Shugabancin Gidan Radio Jalla

Daga Hafiz Mahmoud Kura

shugaban gidan radio JALLa Halilu Ahmad Getso ya bayyana Dalilin da yasa ya ajiye Aikin, Inda yace ya ajiye Aikin ne a radin kansa sabanin jita-jitar da akai ta yadawa cewa sabani suka samu da Mai Gidan Radio Jalla Alhaji Sa’eed Dattijo adahama.

 

halilu ahmed getso ya sanar da hakan ne yau a lokacin da yake jawabin ban kwana a harabar gidan radio jallah fm wanda ke lamba 92 kan titin mission road a unguwar bompai cikin birnin kanon dabo.

 

Alhaji Halilu Getso ya jaddada godiyar sa ga mamallakin tashar redio jallah ALHAJI DR. SA’IDU DATTIJO ADAHAMA bisa damar da ya bashi a matsayin jagoran tashar kuma shugaban gidan radiyon na farko a tarihi…

HALILU AHMED GETSO ya kuma jaddada godiya ta musamman ga ilahirin ma’aikatan gidan radiyon bisa hadin kantda ya samu a lokacin da yake jagorantar gidan radiyon…

 

HALILU GETSO yace yana cike da farin cikin yadda yayi aiki tare da ma’aikata a yanayin girmama juna ba tare da tsegume tsegume ko tauye hakkin kowa ba, don haka sai ya bukaci ma’aikatan tashar da su himmatu wajen bayar da cikakken hadin kai ga duk wanda allah ya kawo musu a matsayin sabon shugaban gidan radiyon..

ya godewa dukkanin tashoshin gidajen radiyon dake kano bisa hadin kan da suka bayar a lokaci da kuma bayan kafuwar tashar ta JALLA FM (lumo akushin allah)

 

ALHAJI HALILU GETSO ya bayyana cewar shine da kansa yaga damar ajiye mukamin sa na MANAGING DIRECTOR JALLA FM

ya ce babu wani laifi da akaimin kuma nima babu wani laifi da na yiwa wani…,illadai kuru a matsayin mu na ‘yan adam zamu iya yn kuskure a ko wanne fanni na rayuwa, don haka idan munyiwa wani ba dai dai ba sai ai mana afuwa…

“ZAN KOMA AIKIN GONA
GADAN-GADAN da kuma sauran aikace aikacen da muka horu akai don neman abinci.”

Tun bayan ajiye Aikin Halilu Getso ake ta yada cewa Wai sabani Suka Samu da Mai Gidan Radio Jalla Alhaji Sa’eed Dattijo adahama

Leave a Reply

Your email address will not be published.