Hajiya sara izzar so, Tarihi, hotuna, Shekaru dakuma Kadara

Hajiya sara izzar so, Tarihi, hotuna, Shekaru dakuma Kadara

Hajiya sara izzar so jaruma ce a Kannywood wadda tasamu karbuwa kuma tayi fice acikin shirinnan Mai farin jini wato Izar so.

Tafitone a matsayin matar Ali Nuhu Wanda aka fi sani da Matawalle duk acikin shirin Na izzar so.

Acikin shirin ta kasance Ita da diyarta wato hajiya Nafisa (Aisha Najamu izzar so) Suna adawa da Lawan ahmad wato (Umar Hashim Mai gaskiya).

 

Tarihin hajiya sara izzar so

Fati Muhammad Adam wadda aka fi sani da Fati Zinariya, ko kuma na ce Hajjiya Sara Izzar so, An haifeta a garin Kano anan ta girma cikin karamar hukumar Nassarawa unguwar Brigade ‘yan tsire, kuma a kano tayi makaranta.

 

Takaitaccen bayani Akan hajiya sara izzar so – Fati Zinariya – Fati muhammad Adam

Sunan asali: Fati muhammad Adam

lakani:            Hajiya Sara izzar so kokuma Fati zinariya

Jihar asali:     KANO

Karamar hukuma: Nasarawa

Unguwa:         Brigade “unguwar yan tsire

Shekaru:        Munakan bincike

Aure:               Babu aure

Hotunan Hajiya Sara Izzar so

Ga kadan daga cikin kyawawan hotunan hajiya Sara izzar so

Hajiya sara izzar so, Tarihi, hotuna, Shekaru dakuma Kadara

Hajiya sara izzar so, Tarihi, hotuna, Shekaru dakuma Kadara

Kadarar Hajiya Sara Izzar so

A halin yanzu bamusan iya abunda jarumar ta mallaka ba, anma muna kan bincike da zarar munsamu bayanai kan kadarar hajiya Sara to zamu sabunta muku wannan labarin.

 

Daga bakin Mai Ita

A wannan bangaren zaku saurari tambayoyi da kuma amsoshi daga bakin jarumar a firarta da jaridar Leadership.

 

Me ya ja hankalinki har kika karkata ga harkar fim?

Abinda ya ja hankalina shi ne, Yadda mutane suke yawan cewa da ma na shiga harkar fim, sabida kwalliyar da nake yi, dan ni akwai kwalliya da diresin kuma ina son hoto toh a wajen hoton ina haduwa da su Dan Ladin Kima suna cewa komai nawa tumach ya kamata na shiga fim, kasan yadda rayuwa take kowa da irin kaddararsa.

 

Ya gwagwarmayar shiga fim din ta kasance?

Gaskiya ba a magana, Saboda ina tsoron mahaifina sosai, tsabar tsoron mahaifina da nake yi Boss ma nake ce masa, kuma kaga ina mugun shiri da Dad dina sosai muna da fahimtar juna, amma dai idan nayi laifi ina mugun tsoronsa, saboda idan na yi laifi ma kafin ma ya ji zancen toh wallahi jikina ne zai fara yin rawa sosai, zan ji hankalina ya tashi gaba daya, saboda bana so abinda zan bata masa rai har ta kai abinda zai kaibya ce zai daken ko zai wani abu. Toh tun a lokacin dai ana taimun maganar shiga fim din, tun abin bai shiga jikina ba har kuma na ji ina son sana’ar, Akwai wani matshi a layin mu irin masu sai da katin nan, idan na yi kwalliya sai ya ce min fosta, ni kuma ba na son sunan raina baci yake, sai wata rana akwai wata antina kozin sista na ce Anti Khadija a Abuja take sai ta zo Kano, sai nake ce mata kin ji wannan sunan ni wallahi ba na son sunan ni ba ‘yar fim ba, ni ba mawakiya ba, ni ba wani abu ba sai na fita wan can gayen ya rinka ce mun wata fosta ni wallahi bana son sunan, sai ta ce ai sunan fosta ba wani abu bane ba, toh haka dai.

 

Lokacin da kika kawo maganar kina son shiga fim, wanne irin kalubale kika fuskanta a dangi musamman yadda a lokacin ba kowa ne ya fuskanci fim ba?

Gaskiya ne, kalubale kuwa ba a magana har ga Allah, kasan shi a rayuwa tarbiyya an ce daga gida ake samun shi, kuma shi daman idan mutum mai tarbiyya ne duk wani hali da za ka shiga a rayuwa ba za ka so wannan tarbiyyar nan taka ta lallace ba, ko kuma ka samu wani sunan da za ka bata gidanku da shi ba. Idan mutum shi daga gidan tarbiyyar ya fito, ko yaya dai sai ka nuna wannan halin. Farko dai ya kamata ta ci gaba da karatu wanne fim kuma?, surutu dai kala kala, toh ni tunda dai iyayena suka lamince mun suka saka min albarka akan sana’ar, “Idan wannan sana’ar da zan shiga da rabona Ubangiji Allah ya sakani a cikin wannan sana’ar, idan kuma ba shi ne hanyar cin abincina ba Ubangiji Allah ya canja min sana’a” tare da addu’o’i ya ce amin” Toh daga lokacin dai duk wani abu na ‘yan uwa tunda iyaye shika shi maka albarka, har iyaye suka yadda duk fitar da za a yi za a ce Allah ya tsare gaba ya tsare baya, Allah ya dawo da ke lafiya. Aka ga dai shekara daya biyu uku dai tafiyarka bai lalace ba, ba ka daina zumunci ba yadda kake dai abun naka dai karuwa yake na girmama mutane da mutumta kowa da wanda ka sani da wanda baka sani ba kowa naka ne, sai kuma su ga ba wani abu da ya canja a kan tarbiyyata, illa ma abun ma karuwa ya yi, shi ya sa abun ma yake ban mamaki wai ace mutum ya shiga fim tarbiyyarsa ta lalace ya zama irin dai abu dai haka rayuwa marasa kyau, toh sai dai daman da wannan mishon din a cikin zuciyarsa.

 

WASU NA KARATUN:

Tarihin hajara izzar so, Hotuna, Kadara da Kuma sunan Asali

Tarihin Minal Ahmad Nana Izzar so, Shekaru, Ayyuka, da Hotuna

Lawan Ahmad phone number: biography, Wife and Net worth

 

Amma dai ga mutum mai fahimta, wanda ya san mene duniya take ciki, toh kuma kake so ka kare mutuncin gidanku, ba zai taba yiyuwa a ce wai za ka shiga sana’ar lalacewa a ce kowa ya so ba wallahi ba zai taba yiyuwa, amma ga mai wayo daga lokacin da ka shiga sana’ar har duniya ta fara ganeka aka gane waye kai, me ya kamata ka yi? ka boye duk wani abu daka san cewa zai taba maka kariyarka ka kiyaye shi, kasan cewa shi wanda ba a sanshi ba sai ya aikata abunda yafi haka ma ya wuce lafiya amma kai fa da aka sani bunka ma fa ake da sharrin baka ma aikata ba, sharrin ma ake binka da shi ballantana ka aikata duniya kuma ta shaida ka ga ka janyo wa kanka bacin rai wanda babu abin da ya kamata ka sakawa iyayenka da shi illah ace yadda ka shiga fim din nan ka fice shi da salama ba wani hau ba wani abu dai daya fada maka, sai ka gode wa Allah, ba dan komai ba ko da ma babu kure ba ka samu komai ba ko ba komai dai atlis iyayenka sa alfahari da kai yadda ka shiga sana’ar Allah ya hada ka da miji nagari ka fita salamun-salamun ka yi aurenka babu babban rufin asiri da ya fi wannan.

Kuma ina tsoron abinda za a ce min yau na aikata abu har ya kai kunnen iyayena ina mugun tsoro sosai.

Me za ki ce game da Jarumin Izzar so wato Lawan Ahmad game da yadda ya sakaki a wannan babba aikin?

Hakane ba abinda zan ce masa, duk da dai na farko shi wannan malami da na baka labari a baya, da nake cewa ya zo ya samu Dad dina ya masa bayani har mahaifina ya amince toh ai shi ne mutumin farko da ya fara hada ni da Lawan Ahmad ka san malamai da malamai sun san junansu, shi ne ya fara hada ni da Lawan Ahmad ya ce toh ga amana dalibata ce kuma ‘yata ce ya bashi amanata tun a lokacin, ni ban san kowa ba dalilin Lawan Ahmad na fara sanin mutane daban-daban ya hada ni da wannan furodusa din, da wannan darakta din yau da gobe har ya zo ya yi min wani fim dinsa mai suna kanwata na manta sunan dai fim din abun ne da yawa ina tunanin kamar haka sunan yake.

Bayan nan kuma ya hada ni da mutane sosai wanda suka sassa ni a fina-finai abokanansa ‘yan uwansa duk dai gashi nan dai, gaskiya ba abinda zan gaya masa sai dai na ce masa Allah ya saka masa da gidan aljannah, babban addu’ar da zan masa kenan, Allah ya raya masa zuri’ansa, Allah ya kara masa zaman lafiya da shi da matarsa da ‘ya’yansa gaba daya, Allah ya bashi arziki dauwamammiya duniya da lahira. Ba zan manta da shi ba kuma ni abinda yake min dadi daman ta wafarsa na fado sai kuma Allah ya sa ta wannan kafar nan nasa kuma Allah zai daga sunana na yi suna a duniya har kowa ya gane ni ya san wacece ni ba zan manta da kai ba Yaya Lawan ina alfahari da kai, ba abinda zan ce maka duk inda kake alkhairin Allah ya kai maka, duk inda kake Allah ya rabaka da masifa ya rabaka da iyayenka duniya da lahari.

Kamar Yadda kike tashe a yanzu, idan miji ya fito za ki iya barin fim ki yi aure?

(Dariya) A guje ma tab! Tabijan ai raya sunnar Manzon Allah (SAW) gaba take da komai, ai ba abin da ya fi aure a duniyar nan, kuma duk wani dan sunnah shi ma zai so ya yi auren sunnah saboda shi ma ya fi dan sunnah ko babu komai na ga ‘yan ‘ya’yayena ‘yan dagwas-dagwas in musu kwalliya in gyara su in gan su tsaf-tsaf! in kale su na ce wannan ‘ya’yana ne? na daga hannu na gode wa Allah, tab! ai wallahi ba abin da nake so yanzu duk duniyar nan babu wani abu da yake gabana babu wani abu da nake so Allah ya nuna min shi da idona a ce yau na bude idona na ganni a gidan mijina auren raya sunnar Manzon Allah (S.A.W), ba ni da alfaharin da ya fi wannan wallahi shi ne babban burina duniya da lahira.

Leave a Reply

Your email address will not be published.