Gwamnatin Jahar Katsina Ta Ba Da Umurnin Sake Buɗe Makarantun Kwana Na Maza

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

 

Gwamnatin jihar Katsina ta umurci da a sake bude Makarantun Kwanan maza jihar a ranar Talata, 2/3/2021.

 

Kwamishinan ilmi na jihar Alhaji Dr. Badamasi Lawal Charanci ya sanar da hakan a lokacin taron manema labarai a Katsina, inda yace za a fara bude makarantun kwana na maza kafin daga bisani a bude na mata nan gaba.

Farfesa Badamasi Lawal ya kara da cewa ana shawartar dukkanin daliban makarantun kwana na jihar da su je makarantun da ke kusa da su. Haka zalika, makarantun ‘yayan jami’an tsaro guda hudu na maza da mata na Mani da Barkiya da Musawa da kuma Faskari za su koma makaranta.

Ku karanta : Sai An Biyamu Diyar Naira Biliyan 450 Zamu Kai Abinci Kudu

Sauran makarantun kwana na mata su dan saurara, za’a nemi su nan gaba kadan, muna bakin kokarin mu ganin daliban sun koma azuzuwan su domin ci gaba da karatun su. Za mu tabbatar an samu kyakkyawan tsaro a makarantu talatin da takwas da muke da su a jihar Katsina, za mu ba da dukkan hadin kai ga jami’an tsaro da ya kamata a shirye muke.

 

Daga karshe ina kira ga al’ummar jihar Katsina da sarakuna da malamai da su ci gaba da dukufa yin addu’o’in samun dawammamen zaman lafiya a jihar Katsina da kasa baki daya.

One Comment on “Gwamnatin Jahar Katsina Ta Ba Da Umurnin Sake Buɗe Makarantun Kwana Na Maza”

Leave a Reply

Your email address will not be published.