Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle na shirin komawa APC gabannin zaben 2023

– Jita-jitar komawar gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle APC kwanan nan ya sake bayyana

– Labarin ya fara ne a shekarar da ta gabata bayan da wani tsohon gwamnan jihar ya bayyana cewa Matawalle na kan hanyarsa ta zuwa APC

– Wasu sabbin rahotanni sun nuna cewa gwamnan zai koma jam’iyya mai mulki nan kusa bayan sasanta jiga-jigan jam’iyyar APC na Zamfara kwanan nan Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya fara shirin komawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

 

Kafin yanzu, akwai jita-jita game da sauya shekar Matawalle, wanda ya zama gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar PDP, bayan hukuncin da Kotun Koli ta yanke kan rikicin da ya biyo bayan zaben fidda gwani na APC a Zamfara.

 

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanata Ahmed Sani Yarima, a shekarar da ta gabata ya bayyana cewa shirye-shirye na gudana kan komawar Matawalle APC. A cewar wata majiya, rikicin da ya dabaibaye APC a jihar na daya daga cikin abubuwan da suka kawo tsaiko ga ficewar gwamnan.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa ana iya kulla yarjejeniyar a ranar Talata, 6 ga Afrilu lokacin da tawagar gwamnatin tarayya za ta ziyarci Zamfara don yi wa gwamnan jaje kan gobarar da ta faru a jihar. Rahotanni sun bayyana cewa gwamnan ya kwashe tsawon watanni yana tattaunawa da akalla gwamnoni biyu na jam’iyyar ta APC.

Leave a Reply

Your email address will not be published.