Gwamnan Bauchi ya Sauke Duk Masu rike da Mukaman Siyasa a jihar

Gwamnan Bauchi ya Sauke Duk Masu rike da Mukaman Siyasa a jihar

 

Daga Abdullahi Maikano

Gwamnan jihar Bauchi Bala Abdulkadir Mohammed ya Rushe Majalisar Zartarwar Jihar da Sakataren gwamnatin jihar, shugaban ma’aikata da sauran masu ba shi shawara na musamman.

Kadaura24 ta rawaito Gwamnan a wata sanarwa da ya fita ga manema labarai ta hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Muktar Gidado ya ce an tube dukkan wadanda aka nada a mukaman siyasa nan take a jihar ta Bauchi.

“Mai girma, Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala A. Mohammed CON (Kauran Bauchi) ya amince da rusa mambobin Majalisar Zartarwa na Jiha da sauran wadanda aka nada mukaman siyasa wadanda suka hada da, Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG)  ), da Shugaban Ma’aikata (COS) Gidan Gwamnati da dukkan Mashawarci na Musamman ”, a cewar Sanarwar.

Sanarwar ta ce mai ba da shawara na musamman kan tsaro da Mai Bada Shawara na Musamman Kan alakar Majalisar Kasa data jiha da Mashawarci na Musamman Kan tallafi Sai Kuma Mai bada Shawara na Musamman kan harkokin yada Labarai da Jama’a ne Kadai za su cigaba da riƙe mukamansu.

“Duk kwamishinoni su mika lamuran ma’aikatun su ga manyan sakatarorin su, yayin da Sakataren Gwamnatin Jiha (SSG), Shugaban Ma’aikata (COS) Gidan Gwamnati da sauran Mashawarta na Musamman da abin ya shafa za su mika ga babban Darakta  Sakatare a gidan Gwamnati “, in ji sanarwar.

Sanarwar ta ambato gwamnan yana godewa dukkan “wadanda aka nada a mukaman siyasa kan irin rawar da suka taka a jihar tare da yi musu fatan alheri a ayyukan da zasu yi nan gaba.”

Leave a Reply

Your email address will not be published.