Gudunmawar Malaman Addinin ce kadai zata Kawo Karshen zaben Gurbatattun Shugabani a Nigeria – Farfesa Auwal Magashi

 

 

Wani Malami a sashin kimiyyar tsirrai na Jami’ar Kimiyya da Fasahar ta Jihar Kano dake Wudil Farfesa Auwal magashi ya bayyana cewa dole sai malaman addini sun bada gudunmawa yadda ya dace wajan wayar da kan al’umma a game da mihimmanci zabar shugabanni na gari a hudubobinsa na juma’a da kuma guraren karatuttukansu .

 

Farfesa Auwal yace Malamai nada gudunmawar badawa wajen Samun mafita a sha’anin Samun kyakyawan shugabanci a matakai daban daban na Kasar nan.

 

“Har yanzu al’ummar mu Suna ganin girman Malaman addinin Kuma Suna Jin maganarsu , don haka Idan suka dauki gabarar fadakar da al’umma irin Shugabanin da ya kamata su zaba”. Inji Farfesa Magashi

 

Farfesa Auwal Magashi ya bukaci matasa da suyi amfani da lokutansu yadda ya dace wajan neman ilimi addini da na zamani , Wanda ta haka zasu sami damar kaucewa fadawa harkokin bangar siyasa .

 

Yace muddin samari suka Samu kyakyawar tarbiyya da kuma wayewar Kai a zamantakewa ta babu shakka za a sami ingantattun shugabanni a nan gaba.

 Professor magashi ya Kuma bukaci al’umma da kowa ya gyara tsakininsa da Allah madaukakin sarki ta hanyar aikata kyawawan ayyuka da kuma kaucewa Abinda Allah ya hana .

Wakilin Kadaura24 ya rawaito Mana Cewa Farfesa Magashi ya Kuma bukaci al’umma dasu dage wajan yin addu’o’i domin samun shugabanni na gari da kuma  zaman lafiya a fadin kasar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published.