Ganduje ya kaddamar da rabon kayan abinchin ciyarwar Azumin bana

Ganduje ya kaddamar da rabon kayan abinchin ciyarwar Azumin bana

Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa

Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da rabon kayan abinchin ciyarwa Wanda aka Saba gudanarwa duk lokacin Ibadar Azumin watan Ramadan.

Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ne ya jagoranci kaddamar da rabon kayan abinchin Wanda za’a gudanar a cibiyoyin ciyarwar guda 150 a fadin Jihar Kano.

Gwamna Ganduje yace an Samar da Shirin ne domin tallafawa Mabukata a Jihar Kano don su Sami saukin yin Bude baki a Nan Kano.

Yace A kowacce rana a duk cibiyoyin da aka ware za’a ciyar da Masu Azumi guda 300 tare da basu man wake hannu da takunkuni saboda magance annobar cutar Corona .

Gwamna Ganduje ya bukaci Shugabanin Kananan Hukumomin kwaryar burnin Kano da su tabbatar da an yi aikin ciyarwar yadda ya kamata ,su kuma Masu karbar Abincin ya bukaci su nuna dattako wajen karbar Abincin.

 

Gwamnan ya Kuma ce ya Sanya jami’an Hukumar karbar koke-koke da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano dasu Sanya idanu domin tabbatar da anyi aikin ciyarwar cikin gaskiya da adalci.

Wakilinmu na fadar gwamnatin jihar Kano Yakubu Abubakar Gwagwarwa ya rawaito Mana cewa a Jawabinsa kwamishinan Kananan Hukumomi na jihar Kano Murtala Sule Garo yace a Wannan Shekara za’a raba a buhun shinkafa Dubu 4,300 sai Gero buhu Dubu 1,260 wake Dari 840 sai buhun fulawa guda 840 da Kuma Sikari Dubu 1,260 da dai sauransu .

Murtala Sule Garo yace a Wannan karon gwamnatin jihar Kano ta Kara adadin kudaden da ake kashewa wajen ciyarwar Azumi domin Kara baiwa mutane da yawa damar amfana da Shirin.

Leave a Reply

Your email address will not be published.