Duk da Umarnin Kotu Yan Majalisar Zamfara na son tsige Mataimakin Gwamnan

Duk da Umarnin Kotu Yan Majalisar Zamfara na son tsige Mataimakin Gwamnan

 

Wasu ‘yan majalisar dokokin jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya sun sha alwashin tsige mataimakin gwamnan jihar Mahdi Aliyu Gusau bisa zargin saba doka.

Hakan na zuwa ne bayan da mataimakin gwamnan ya ki bayyana a gaban majalisar kamar yadda ta buƙaci ya yi don amsa tambayoyi.

Mataimakin gwamnan ya kafa hujjar cewa tuni kotu ta umurce su da su dakatar da gayyatar da suke masa.

 

Mahdi Aliyu Gusau: Allah Ya ba ni girma na zama jagoran PDP a Zamfara
Jihar Zamfara: Majalisar Dokokin jihar ta gayyaci mataimakin gwamna
Rashin Tsaro: Mata da yara sun yi zanga-zangar rashin tsaro a Zamfara
Honorabul Yusuf Alhasan Muhammad Kanoma, mai wakiltar Maru ta arewa a majalisar, ya shaida wa BBC cewa Mahadi Aliyu Gusau ya saɓa ƙa’ida shi ya sa suka ga ya dace su tsige shi.

 

“Da farko ya shirya taron siyasa duk da kwamishinan ƴan sanda ya ce mishi kada ya yi, saboda a jajiberin taron an kashe kusan mutum 54 a Faru da Gora, amma bai saurari wannan shawara ba ya gudanar da taron.

“Bayan nan ne muka ga ya dace mu gayyato shi ya amsa tambayoyi, kuma abin damuwa baya ga wannan ma ya tara mutane yana zage-zage. Abin kunya ne a ce mataimakin gwamna na jiha ya zo ya yi wannan,” a cewar Honorabul Yusuf Kanoma.

 

Ya ce kamata ya yi a ce mataimakin gwamnan na alhinin kashe mutanen da aka yi.

Ɗan majalisar ya ce takardar da kotu ta aike ta dakatar da su daga gayyatar mataimakin gwamna ta daina aiki ranar 28 ga wata amma sun sake gayyatarsa ran 29, ya ce kuma Mahadi Aliyu Gusau ya sa hannu kan wata takarda da ya aike wa majalisar ta amsa gayyatarsu.

 

Ya ce a halin yanzu kwamitin harkokin shari’a na majalisar na nazari kan takardar kuma za su gabatar da rahotonsu ga majalisa inda daga nan ne za a ɗauki mataki na gaba.

Sai dai Honorabul Yusuf Alhassan Kanoma ya ce idan mataimakin gwamnan zai bayyana a gaban majalisar suna iya yafe masa laifin da suke ganin ya yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.