Dattawan Arewa sun aikewa CBN koke kan wariyar da ake nunawa Arewa na tallafin kudi

Kungiyar dattawan Arewa ta ACF ta aikewa da CBN koke kan nunawa yankin wariya da ake kan tsare-tsaren kudi na gwamnatin tarayya.

 

Tace tsare-tsaren basa amfanar Arewa kamar yanda ya kamata a matsayin ta na yankin da yafi kowane yawan al’umma.

Kungiyar tace gwamnati ta ware banki 1 wanda mallakinta ne take amfani dashi wajan bayar da kudin tallafi wanda kuma sauran kananan bankuna masu zaman kansu na shan wahala wajan samun irin kudin da wancan bankin ke samu.

Suka ce kananan bankuna na tallafawa mutane da karfafa sana’arsu dan hakane suke neman CBN ya sake duba dokokin da ya saka akan bankunan dan zasu sa da dama bankunan arewa su durkushe.

One Comment on “Dattawan Arewa sun aikewa CBN koke kan wariyar da ake nunawa Arewa na tallafin kudi”

Leave a Reply

Your email address will not be published.