Dana san haka harkar fim take da ban shige ta ba – sarkin waka

Dana san haka harkar fim take da ban shige ta ba – sarkin waka

Bayan mutane suna ta cece kuce akan fitar jaruma Nafisa Abdullahi daga shirin labarina kawai sai munkayi kicibis da wani rahoto kuma a shafin jaridar dimokuraɗiyyar a facebook sun wallafa labarin cewa sarkin waka ya fara dana sanin shiga harka fim.

 

Dana san haka harkar fim take da ban shige ta ba – sarkin waka

Dana san haka harkar fim take da ban shige ta ba – sarkin waka

“Mawaƙin masanaantar Kannywood Naziru Ahmad wanda ake yiwa laƙabi da Sarkin waka, yash alwashin cewar daya san haka harkar fim take da bai shige ta.

 

Yana mai bayyana haka ne a wata tattaunawar sa da manema Labaru a babban birnin tarayya Abuja.

 

Yace gaskiya daya san haka harkar take da bai shigeta ba, yace rashin lokacin sanaar ne yake damun sa.

 

Shi ya saba tashi ne karfe 1pm na tsakiyar rana, yanzu kuma daya shiga harkar Fim karfe 9 ake fara daukar fim, kuma sai karfe 6 na yamma ake tashi, rashin lokacin bacci a harkar fim gaskiya yana takura shi.

 

Kazalika yace da alama dai yana ganin zai hakura da shirin fim kwata-kwata, zai cigaba da harkar sa da aka san shi da ita.”

Leave a Reply

Your email address will not be published.