Da duminsa: ‘Yan bindiga sun kutsa kotu, sun yi awon gaba da alkali a Katsina

Miyagun ‘yan bindiga sun kutsa zauren kotu a kauyen Bauren Zakat dake karamar hukumar Safana ta jihar Katsina

Sun yi awon gaba da alkalin kotun mai suna Alhaji Husaini Samaila a ranar Talata wurin karfe 3 na yammaci

Kamar yadda aka gano, gwamnati ta mayar da kotun zuwa karamar hukumar Safana ne saboda rashin tsaro

 

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da alkali a cikin kotun Sharia dake kauyen Bauren Zakat a karamar hukumar Safana ta jihar Katsina.

Kamar yadda ganau suka sanar da Daily Trust, maharan sun balle kotun inda suka shiga wurin karfe 3 na yammacin ranar Talata kuma suka yi awon gaba da alkalin mai suna Alhaji Husaini Sama’ila.

An mayar da kotun shari’ar ne karamar hukumar Safana saboda dalilan tsaro.

Har yanzu dai ba a san dalilin da ya kai alkalin kotu ba duk da yajin aikin da kungiyar ma’aikatan shari’a na Najeriya (JUSUN) ke ciki.

KU KARANTA : ‘Yan bindiga da suka yi garkuwa da malamai a Birnin Gwari sun nemi N15m

Katsina tana daya daga cikin jihohin yankin arewa maso yamma da ‘yan bindiga suke cin karensu babu babbaka.

Har a halin yanzu jami’an tsaro basu yi martani kan aukuwar lamarin ba.

Idan zamu tuna, Legit.ng ta ruwaito cewa ma’aikatan shari’a sun shiga yajin-aiki, har an kai ga rufe kotu da-dama a Najeriya.

Shugaban kungiyar malaman shari’a na bangaren jihar Legas, Kehinde Shobowale Rahamon, ya bayyana abin da ya sa ma’aikatan su ka tafi yajin-aiki.

Mista Kehinde Shobowale Rahamon ya ce har yanzu doka ta 10 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa hannu a kai ba ta fara aiki ba har yanzu.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.