Bidiyo: Diyar biloniya Dangote, Halima Dangote ta gigita masu kallo da salon rawanta

Halima, diyar hamshakin mai arzikin Afrika, Aliko Dangote, ta sanya masoya cikin shauki mai yawan gaske

 

Bayan Halima taje wani taro, ta burge jama’a da wani salon rawarta mai kayatarwa da rikitarwa

 

Bidiyon rawar da tayi ya karade kafafen sada zumuntar zamani yayin da jama’a suka yi ta tsokaci

 

Diyar attajirin dan kasuwar nan, Aliko Dangote, Halima, ta zamanto abar labari a kafafen sada zumuntar zamani domin ta burge jama’a kwarai.

 

Matar mai karancin shekaru wacce kowa ya sani da matukar tsantseni da kamun kai ta bayyana tana kwasar rawa mai daukar hankali a wani taro da ta je.

 

 

Ba kamar yadda ake zato ba, cikin kwarewa Halima ta bayyana a fili tana rawa tare da bin wakar wani mawaki sanannen mai suna Teni, cike da shauki.

Ko kadan ba a hango tsoro ko shakka tattare da Halima ba domin cikin kwarewa ta kwashi rawar. Take a nan masoya cike da shauki da begenta suka yi ta yada bidiyon Halima Dangote tana rawar wacce ta tafi da tunaninsu har da damansu suke tsokaci iri-iri akai.

Leave a Reply

Your email address will not be published.