Barayi sun afka gidan jarumin Kannywood, sun yi awon gaba da sabuwar motarsa da wasu muhimman kayayyaki

– Barayi sun kai farmaki gidan wani jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Nasiru Bello Sani

 

– Yan bindigar sun kuma sace sabuwar motar da ya saya kirar SUV da sauran kayayyaki masu daraja

 

– Jarumin wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya yi godiya ga Allah kasancewar basu taba kowa ba Wasu barayi dauke da muggan makamai sun shiga gidan wani fitaccen jarumin fina-finan Kannywood, Nasiru Bello Sani, wanda aka fi sani da Nasiru Naba da misalin karfe 1:00 zuwa 2:00 na safiyar Laraba. Sun kuma yi awon gaba da sabuwar motar da ya saya kirar SUV da sauran kayayyaki masu daraja.

Leave a Reply

Your email address will not be published.