Ba’a arziki da aikatau – Dr. Zahra’u Umar

Ba’a arziki da aikatau – Dr. Zahra’u Umar

 

Daga Ummukursum Murtala

Kwamishiniyar harkokin mata da walwalar al’umma ta jihar Kano Dr Zahra’u Muhd Umar ta Bukaci Iyaye su daina tura ‘ya’yansu aikatau domin yin hakan bashi da Wani alfanu ga yaran.

Kwamishiniyar ta bayyana hakan ne Cikin Wani sako da Jami’ar Hulda da jama’a ta Ma’aikatar Mata Bahijja Malam Kabara ta aikowa Jaridar Kadaura24.

 

Malama Zahra’u Muhd tace ba’a taba Samun Mara Ilimi ya taka wani Matsayi ba a tarihin Duniya.

“Duk Shugabanimu da Gwamnonin da sanatocinmu ba’a taba Samun Wanda yayi aikatau a cikinsu ba , Rayuwa sukai da abun da Allah ya horewa Iyayen su” Dr Zahra’u Muhd

Kwamishiniyar ta Bukaci Iyaye da su Rika tawakalli da halin da Allah ya Barsu a ciki, talauci ba uzuri bane da za’a hana yara Ilimi a turasu aikatau ba.

 

Yace buri da bukatu na karya ne suke sawa Iyaye suke tura ‘ya’yansu aikatau wai don su Sami abubuwan da zasu biyawa yaran bukatunsu na aure ko wani Abu.

Kwamishiniyar tac a Musulunci Haramun ne Iyaye laru da cewa ‘ya’yansu kanana Waɗanda basu balaga sune zasu dau dawainiyarsu ,tace kamata yayi Iyaye su dau dawainiyarsu’ya’yansu Haka addini yace “Inji Dr Zahra’u Muhd.

Leave a Reply

Your email address will not be published.