Ayyiriri ku kalli wanda Hadiza Gabon ta fidda a matsayin mijin aure

Ayyiriri ku kalli wanda Hadiza Gabon ta fidda a matsayin mijin aure

 

A safiyar ranar alhamis ne rahotanni suka rika yawo a kafafen yada labarai da sadarwa, a kan cewa shahararriyar jarumar fina finan Hausa ta Kannywood Hadiza Aliyu Gabon ta fitar da wanda za ta aure.

 

Wannan dai shi ne hoton saurayin da ta fitar wanda ake kyautata zaton cewa, za ta yi wuf da shi, masoya jarumar dai sun dade suna zuba ido don ganin wanda za ta aura amma a halin yanzu za’a iya cewa aski ya zo gaban goshi.

 

Sashin hausa na APA dai yayi ta yunkurin tun tubar jarumar da wayar salula domin jin ta bakin ta dangane da wadannan rahotanni da ke yawo, amma hakar mu bata cimna ruwa ba domin kuwa lambobin wayarta ba sa tafiya gabanin hada wannan rahoto.

 

Awani Labarin : Hadiza Gabon ta yi magana a kan soyayya, ta fadi abin da ya fi komai ba ta sha’awa a rayuwa

 

 

Amuna fatan Allah ya tabbatar da alheri.

Leave a Reply

Your email address will not be published.