An harbe wani babban malamin addinin Musulunci a gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.
An yi wa Sheikh Ali Amini, ruwan albarussai yayin da yake jagorantar sallar Asham a ranar Asabar a cikin babban masallacin garin Beni.
Har yanzu dai ba a bayyana waɗanda suka aikata kisan ba.
Tun da farko wasu da ake zargin ‘yan tawayen ADF ne sun kai hari kan wasu ƙauyuka biyu a yankin.
Rahotannin da ba a tabbatar da su ba sun ce an kashe mutane 19 ciki har da sojoji da dama.
Yayin da ƴan ƙasar ke ƙara fusata kan yawaitar hare-haren ƴan tawaye, shugaban kasar Felix Tshisekedi a ranar Juma’a ya ayyana wani mataki na yi wa lardunan Arewacin Kivu da Ituri ƙawanya- matakin da ake ganin zai bai wa sojojin Congo karin karfi da ƙwarin gwiwa.