An Haramta Wa Masu Digirin Kwatano Zuwa NYSC

Hukumar lura da masu hidimar kasa, NYSC, ta haramtawa daliban da suka kammala wadansu daga cikin jami’o’in kasashen waje musamman na Jamhuriyyar kasar Benin da na Nijer da Kamaru zuwa hidimar kasa ta 2021 da za a yi.

 

An zargi jami’o’in da kammala digirinsu a cikin watanni, wanda har ‘yan Nijeriya ke kiran irijn wannan digiri da ‘Digiri dan Kwatano’.

 

A wata takarda da NYSC ta aikawa shugabannin lura da hidimar kasar ta Abuja, dauke da kwanan watan 5 ga watan Maris din 2021, ta nemi da ka da su amince da kowanne dalibi da ya kammala digiri daga wadancan kasashen, dalilan da NYSC din ba ta bayyana ba.

 

Sannan ta nemi dukkanin shugabannin lura da hidimar kasar, da kuma sashen tabbatar da ingancin digirin kasashen waje da su lura da wannan.

 

Jami’o’in da wannan lamari ya shafa su hada da; Al-Nahda International University (Niger Republic); Ecole Superieur Sainte Felicite (Benin Republic); Ecole Superieur D Administration et DEconomics (Benin Republic); Ecole Superieur DEnseignement Professionelle Le Berger – ESEP Le Berger (Benin Republic) da; Ecole Superieur St. Louis DAfrique (Benin Republic).

 

Sauran sun hada da; Institute Superieur de Comm. Dord Et De Management – ISFOP (Benin Republic) da kuma International University, Bamenda (Cameroon).

Leave a Reply

Your email address will not be published.