Amurka ta bai wa Najeriya wa’adin sa’a 24 ta mika mata Abba Kyari

 

Amurka ta bai wa Najeriya wa’adin sa’a 24 ta mika mata Abba Kyari

 

Shugaban hukunar leken asiri da binciken miyagun laifuka ta Amurka Federal Bureau Investigation wato FBI a kaice Mr. Christopher A Wray ya nemi hukumomin tsaron Najeriya da su mika jami’in dan sandan nan Abba Kyari nan da zuwa sa’a 24 ga hukumar domin ta ci gaba da bincikensa don samu cikakkun bayanan da take zargin akwai a wajen sa.

Shugaban hukumar ya ce, FBI ba zata hukunta Abba Kyari ba matukar bada same shi da hannu a laifin da take zarginsa da aikatawa ba, tun a karshen makon daya gabata ne dai hukumar ta FBI ta zargi gwarzo kuma hazikin dan sandan na Najeriya wanda ya kware wajen kama masu aikata miyagun laufuka a kasar da laifin kulla alaka da Hushpuppi wani kwararren dan damfara da kuma dan Najeriya, da hukumar ta kama.

Sai a bangare guda Abba Kyari na ci gaba da samun goyon baya musamman ga al’ummar arewacin Najeriya a baya bayanna ma wani bawan Allah ya yi wannan rubutun a kan sa kamar haka.

BUƊAƊƊIYAR WASIKA ZUWAGA YAN AREWA

Musani DCP Abba kyari dan arewa ne kuma yana daga cikin manyan gwarazan dake son kawo karshen ta’addancin dake addabar kasarmu.

Daga Ismail Ibrahim Gusau

Amma muda kanmu muke bada dama anason cin zarafin dan uwanmu dan arewa, idan mukayi duba da abunda yafaru kwanan nan yakamata muma mutsaya tsayindaka domin kare martabar .jarumin yankinmu.

Sunday Adeyini Adeyemo(igboho) kowa yasan dan kudu ne mai iƙirarin kafa ƙasar yarabawa jami’an tsaro na farin kaya(DSS) sunyi nasarar shiga cikin gidansa sunkama makamai da gurɓatattun kaya, amma duk da haka yan uwansa yarabawa ƙoƙarinsu suga sunkare dan uwansu, akwai ƙungiyar yarabawa(Afenefere) suma burinsu suga anyima Sunday Igboho adalci.

Akwai Mazi Nmandi kanu shima kowa yasani yana iƙirarin kafa ƙasar inyamurai sannan ankamashi da laifin ta’azzara jama’a wajen kawo tashin hankali cikin kasa amma manyan yankinsa suna bada gudunmawa wajen kare dan yankinsu.

Miye amfanin mu idan muka zura ido anayi muna ɗauki ɗai-ɗai wannan babban ƙalubalene ga yan arewa, munada manya a cikin arewa sunaji kuma suna gani amma sunyi shiru.

Allah yaqara inganta yankinmu na arewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.