Addu’ar muce ke bin Maryam Yahaya – Inji Wata Budurwa

Wata budurwa mai amfani da suna Fatimaumsiun a shafinta na TikTok ta wallafa wani bidiyo wanda wani ma’aboci amfani da Facebook, Sada bn Suleiman Usman ya kwafo ya wallafa a shafinsa ta ce kanwar wannan saurayin da a bara ya wanko kafa tun daga jihar Yobe har Kano don ganin jaruma Maryam Yahaya.

 

Addu’ar muce ke bin Maryam Yahaya

 

Addu’ar muce ke bin Maryam Yahaya

 

Budurwar wacce ta ke magana cike da takaici inda har sautin kukanta aka dinga ji yana fita ta ce alhakinsu ne ya kama jarumar har ta fadi mummunan ciwon da ta rame kuma halittarta ta sauya.

 

Kanwar Saurayin da ya sha fiya-fiya saboda Maryam Yahaya ta ce alhakinsu ne ya kama jarumar

 

Idan ba a manta ba, jarumar ta fadi ciwo wanda har yanzu ba ta dawo yadda take ba inda aka ga ta rame, rama mafi muni wanda har wasu su ke yi mata izgili idan ta wallafa hotunanta a kafar sada zumunta.

 

Sai dai a bangaren budurwar, ta ce ta yuwu addu’arsu ce ta kama jarumar don ta nuna musu rashin imani.

Leave a Reply

Your email address will not be published.