Abinda yasa na dawo fim – Fati Muhammad

Jaruma fati Muhammad wanda tayiwa masana’antar kannywood yaji fiye da shekara goma sha uku 13 da yan watanni ba’a sake ganinta ba a cikin masana’antar ba.

 

Jarumar fati Muhammad ta bayyana dalili da yasa ta dawo shine domin masoyanta sunyi ta kiraye kiraye domin ta dawo masana’antar amma sai yanzu ta karba kira wanda hakan yasa sunji dadi.

 

Shin ko miya jawo hankalin ki na dawo harka fim yanzu?

Eh dalilina shine nayi shawara da Ali Nuhu kuma ya bari kwarin gwiwa sosai wanda yanzu haka zai shirya sabon fim da zan fito a cikinsa kuma yanzu haka ana daukar gidan danja dani zango na biyu.

 

Shin ko yah kinkaji game da hotonki da ake yadawa da cewa kin tsufa?.

Alhamdulillahi tunda har Allah yasa na samu tsawon rai da na tsufa domin tsufa dole ga kowa duk wanda yayi tsawon rai, hotunan nayi kwaliya ne na shiga taro sai nayi dumi wanda dole kwaliyata ta chaɓe ko kadan banji zafin wannan hotunan da ankayi yadawa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.