A Dalilin fina-finan Hausa na Musulunta – inji Wata Yar Wasan Hausa

A Dalilin fina-finan Hausa na Musulunta – inji Wata Yar Wasan Hausa

 

Daga Nasiba Rabi’u Yusuf

Wata Jaruma a masana’antar Kanywood Mai Suna Rahma A Ibrahim wadda ita ce ta fito a matsayin Jaruma a Cikin wani Shirin Mai Dogon zango Mai Suna Jamila Makira ta bayyan cewa ta Musulunta ne sanadiyyar fina-finan Hausa da take kallo.

Rahma wadda akafi Sani da Rahma kumo ta bayyana hakan ne Cikin Wata Zantawa da sukai da Majallar Matashiya Tv.

 

Tace fina-finan Hausa Suna taimakawa sosai wajen fadakarwa tare da Ilimantar da al’umma duba da irin sakonni da sake kunshe Cikin Fina-finan.

” Daga Cikin Fina-finan da suka sa na Musulunta akwai Ahalulkitab, Ga duhu ga haske da Kuma Asahabul kahfi” inji Rahma Kumo

Rahma tace ganin irin Gudunmawar da fim din Hausa ya bani, shi yasa Nima na shiga Harkar don na taimakawa Wasu su fita Daga Cikin duhun da suke ciki.

 

” Gidanmu Gidan Malaman addinin kirista ne, muna da alqur’ani na turanci dana Hausa Idan kalli fim naji an karanta ayar alqur’ani nakan je na duba a Cikin Wanda muke dashi Kuma na kwatantashi da baibule to da Haka na gana fahimci addini Musulmci” inji Rahma Kumo

Tace bayan ta fahimci addini Musulmci ta shiga Cikin da ne ta hannun Wani Malami a unguwar su.

Rahma Kuma Wadda tace ita har asalin Karamar Hukumar Kumo ce dake jihar Gombe tace ta shiga fim ne don ta bada tata Gudunmawar domin cigaban al’umma

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.